Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

MAGANIN LAULAYI GA GAMASU (JUNA BIYU) INSHALLAH



 MAGANIN LAULAYIN MASU CIKI JUNA BIYU FISABILILLAHI

                 


(JUNA BIYU)


Laulayin ciki abu ne wanda yake zuwa bisa yanayin halittar da Allah ya yiwa matar.

Domin akwai bambanci a tsakanin su kansu matan, wata matar tafi wata shan wahala a lokacin laulayi.


*Ga wasu magunguna nan a nema a hada, InshaAllah za a dace:*


(1)Ganyen Na'a-Na'a (Fresh ko busasshe mai kyau).

(2)Lemon tsami.

(3)Zuma mai kyau.

(4)Citta da Kanumfari.


A dafa ganyen Na'a-Na'a kamar cikin tafin hannu 2 a cikin ruwa kofi 3, a zuba citta da kanumfari daidai misali a dafa su tare.

Idan an sauke, an tace ruwan sai a zuba zuma gwargwadon yadda ake so, sannan a yanka lemon tsami guda biyu (me ulcer Rabi), a matse a cikin ruwan da aka dafa din sannan asa a flacks ana sha kadan kadan wuni daya a shanye za'a samu sauki.


*AMFANI*

Mai Juna biyun za ta samu qarfin jiki, za ta dena yawan zubar da yawu (Miyau) da hararwa (amai) kuma jaririn dake cikinta zai samu kaifin basira da kwakwalwa.


Allah ya sauki dukkan masu juna biyun Musulmai Lafiya. Wadanda aka haifa kuma Allah ya raya mana su.

Marasa yara Allah ya basu masu albarka. 

Mata masu planning kafin aure ku kiyaye akwai nadama sosai. 

 *Momyn Aslam & meenat😍*




Post a Comment

0 Comments