Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

MUHIMMAN BAYANAI GA IYAYE GAME DA TARBIYYAR YARANMU

 


Nasiha Domin Tarbiyar 'Ya'yan Musulmi...


  1. ka yaba mawa yaro ko da kuwa ya samu 4/10 a jarrabawa ne, yabi yaronka a gaban sa zai samu karfin gwiwar  samun 10/10 jarabawa ta gaba ba fada zaka masa ba.


  2. Duk lokacin da za ku yi magana da yaranku, ku yi magana cikin girmamawa, ku ce "Jazakallah khairan", da dai sauransu. Yi amfani da 'don Allah' wajan magana da su kada ku ya waita rantsuwa a gaban yaran ku.


  3. kar a dauke ma yaro lokacin wasa ta hanyar ko da yaushe karatu bashi da hutu,  Idan ka yi haka, za su yi tawaye a rayuwa.


  4. Ku taimaki yaranku wajen tsaida shawarwarin ku. Yi musu jagora ta hanyar magana da su. Idan suna son yaro ya Kai wani mataki arayuwa, to a taimaka musu su tsara shi yadda tsarin musuluncin ya tsara.


  5. Ka tambayi yaron ka ra'ayin sa. Misali, idan za ka sayi mota, tambaye sa wanne launin motar suke son asiya. Wannan yana haɓaka dabi'ar shawarwari a cikin ya'ya.


  6. Keɓe kusurwar gidan ga ɗanku kuma ku rubuta sunan ɗanku a wurin - sanya shi ɗan sarari. Hakan zai sa su kara amincewa da kansu.


  7. Koyawa yaro binka a sallah, hanya ce mafi ƙarfi kuma Mai kyau. Yaron ku zai tuna abin da ya gan ku kuna yi har abada. Fara koya musu karatun sallah tun suna shekara


  8. Ka ƙarfafa yaran ka suyi tambayoyi. kai kuma kayi ƙoƙarin amsa kowace tambaya yadda zasu fahimce ka. ka yabe tambayoyinsu a wasu lokuta.


  9. Ka cika alkawuran da ka yi wa ‘ya’yanka. Kada ku yi manyan alkawuran da ba za ku iya cikawa ba; Hakan ya zai sa su zama masu al’adar yin alkawuran ƙarya. Idan kun kasa cika kowane alkawari, bayyana musu gaskiya.


  10. Ku yiwa yaranku addu'a. Ko da sun yi kuskure, ka yi musu addu'a.


  11. Faɗa musu ba ko da yaushe bane ake yin nasara ba raywa tana da kalubale, amma kada ku yanke bege. Koyar da su yadda za su mayar da martani domin samun nasara.


  12. Ka nemi gafarar yaronka idan kayi kuskure, wannan yana koya wa yaronka tuba ga Allah. Kada ku yi izgili idan kun yi kuskure.


  13. Ka yabi kyawawan ayyukansu, ka ba su kyauta, ka bayyana musu cewa wannan kyautar ta alheri ce da ka yi.


  14. Ku tabbata kun horar da yaranku karatun Alqur'ani a kullum, gwargwadon karfinsu.

  15. Ka rika gaya wa yaranka cewa kana son su, ka gaya musu irin kyawunsu da yadda suke da muhimmanci a gare ka, ka rungume su, sumbatar yaranka sunna ce.

   Allah yashirya mana zuri'a bakidaya🤲🏻



 ```By Chef Oum Aslam & meenat👩🏻‍🍳```

Post a Comment

0 Comments