A maimakon badda makudan kudade wajen sayen mayukan kara gashi da hana zubewar shi , za ’ a iya amfani da ganyen gwava wanda bincike ya nuna cewa ya fi karfi da inganci akan yawancin kayan gyaran gashin da ake sayarwa na kamfani .
Ganyen gwava na dauke da sinadaran da ke kara yawan gashi , ya tsaida zubar shi , ya kuma kara mashi lafiya da sheki .
Ga yadda ake amfani da shi : Za’ a dafa ganyen gwava kamar cikin hannu ko damka daya a cikin lita daya na ruwa , sai a barshi ya tafasa na tsahon minti 20 , sannan sai a sauke a barshi ya huce .
Idan ya huce za ’a matse ganyen a tace ruwan .
Wannan ruwa shi za ’a mursuka cikin gashin tundaga kasa Ko dai a mursuka ruwan bayan an wanke gashi a barshi na tsahon awanni sannan a wanke , ko kuma a mursuka shi da daddare , a rufe da hular leda a kwana da shi .
Idan aka ci gaba da amfani da Ganyen gwava , za ’a ga banbanci .
Gashi zai kara laushi , ya karfafa , sannan ya daina zuba, al ’amarin da zai sa shi ya kara tsaho cikin dan kankanin lokaci.
By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳
0 Comments