Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKU RABUDA NANKARWA (STRETCH MARK)


 HANYOYIN MAGANCE NANKARWA


   RUWA

Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri.


MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA ACIKIN KO WACCE RANA


Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe.

Kofi daya bayan karin kumallo

kofi Daya Kafin azahar kisha

kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci.

kofi daya da la’asar.

kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci.


MAN CIKA-GIDA (CASTOR OIL)


Wannan man yana da Matukar amfani wajen magungunan da suka shafi fata kamar maganin pimples, cin zanzara, tabbai da sauran su.


YANDA AKE AMFANI DASHI


Ki dibi kadan sai ki sa a wuta yayi dumi sannan ki shafa a duk inda kika san yana da nankarwa ajikin ki da dumi duminsa ba yanda zai kona ki ba. Kiyi hakan har na tsawon wata guda.


Ko kuma ki shafa man sannan ki dauko yadi mai taushi na cotton ki rufe wurin dashi ki Zuba ruwan dumi a gora ki riqa dorawa a saman yadin.


ALOE VERA

Ki tatse farin ruwan aloe vera kullum ki riqa shafawa a wurin idan ya bushe sosai sai ki wanke da ruwan dumi Ko kuma ki diba man aloe vera din chokali daya ki hada da vitamin E oil capsule daya ki shafa a wurin.


FARIN KWAI

K fasa Kwai daya ki cire kwaiduwan kwan ki yar sai kiyi amfani da fork ko whisker kiyi ta kada farin kwan har sai yayi kauri ya yi fari tas kamar cream sannan ki shafa a wurin nankarwan ki barshi ya bushe sannan ki wanke da ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu.


RUWAN LEMON TSAMI

ki matse lemun tsami sai ki diba ruwan ki riqa shafawa in circle a inda nankarwan suke har sai kinga ya bushe ki barshi bayan minti goma ki dauraye da ruwan dumi. Ko kuma ki hada ruwan lemun da ruwan nukakken cucumber sannan ki shafa.


SUGAR

Ki hada suga da almond oil ko zaitun ko man kwakwa da ruwan lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan ki shiga wanka.


RUWAN DANKALI

Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki shafa ruwan a inda nankarwan take idan ya bushe zaki ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko zaitun ko man kwakwa.


MAN KADE

yawan shafa man kade a wurin ma yana rage shi sosai. Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zaran sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ce babu kemikal acikin ta dan haka yana daukan lokaci kafin aga canji kamar Sati biyu idan baki ga chanji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shine masani. Allah yasa mu dace


MAGANIN NARKARWA

1.ruwan khal farin,ki shafa a gurin for 15mins sai kiyi wankan ki,inkin dawo kuma,sai kishafa ma gurin man kwakwa,insha Allahu zai bace kuma skin naki zaiyi kyau.


By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻‍🍳



Post a Comment

0 Comments