*ABIN DA YA FI SAURIN KAI MATA GIDAN ALJANNA*🍃🍃
Bayan imani da Allah da Biyayya ga Manzon Allah SAW, babu wani abu da yake saurin kai mata shiga aljanna kamar:-
BIYAYYA DA KYAUTATAWA MIJIN TA.Ki nemi yardar mijinki ta hanyar kyautata masa da kalamai masu dadi da aiyukan ibadar aure yin hakan zai shigar da ita aljanna insha Allah.
Aiki dan kadan marar wahala zai janyo maki dauwama acikin aljanna.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
(Shin bazan baku ba labarin Mata yan aljanna ba daga cikin ku?Mata masu yawan haihuwa wadanda suka iya soyayya,wadda idan tayi maka laifi zata dora hannunta akan naka,sannan sai tace ga hannuna nan akan hannunka bazan dauke hannuna ba akan naka ba har Sai ka daina fishi dani har sai ka yafe min).
@السلسله الصحيحه 3380.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
(Idan mace ta sallaci sallolin guda biyar na farilla,kuma tayi azuminci azuminta na farillah,kuma ta kiyaye farjinta daga zina,KUMA TAYI BIYAYYA DA KYAUTATAWA MIJINTA,za'ace da ita kishiga aljanna ta dukkan kofar da kikaga dama)
@صحيح الترغيب 1932.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
(Baya halasta ga mace da tayi azumin nafila alhalin mijinta yanana har sai da izininsa)
@صحيح ترغيب 613.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
(Idan mutum ya kirayi matarsa zuwa shimfidarsa sai taki :wa,ya kwana yana mai fishi ita,Mala'iku suna la'antarta har zuwa ta wayi gari)
@صحيح مسلم 1434.
Allah ne mafi Sani.
اللهم أصلح أحوالنا أجمعين
By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳
0 Comments