Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

HANYOYIN WANKE HAKORA SUYI TAS MURMUSHI KO INA BABUJIN KUNYA


 HANYOYIN WANKE HAKORA SU YI HASKE, MURMUSHI KO INA BA JIN KUNYA


Mutane da dama sun tafi a kan ganin wata kala a hakora ba farar kala ba, alamu ne na kazanta, a inda wasu kuma al'ummar sun tafi a kan ganin ja ko yaluwar kala a kan hakora shi ne wayewa. 


A yau za mu yi nazari ne kan wasu hanyoyin masu sauki na wanke hakora su yi haske da sheki InshaAllah kamar haka:-


*HANYA TA 1:-*

A samu danyar citta a goge ta kamar cikin karamin cokali, a saka a kan brush ana goge hakora a hankali kamar minti 5 sai a kuskure baki tsawon sati daya. 


*HANYA TA 2:-*

A samu lemon tsami rabi a matse ruwan sa, asa gishiri kadan ana dangwala da brush ana goge hakora sati daya. 


*HANYA TA 3:-*

A samu baking soda a dangwala da brush ana goge hakora sati daya shima na haskaka shi da sheki InshaAllah. 


*HANYA TA 4:-*

A samu ruwan hydrogen peroxide ana dangwala kadan da brush ana goge hakora sati daya za aga canji. 


*HANYA TA 5:-*

Bayan gama wanke baki da kowanne irin man wanke baki sai a dangwali man kwakwa original a kara wanke hakora shi wannan koda yaushe ana iya yi bashi da illa ga dadashi. 


*HANYA TA 6:-*

Ga masu matsalolin ciwon hakori da dafewar su harda warin bakin da ba daga hunhu yake fita ba, ana samun kanumfari da gawayi a dake guri daya ana wanke hakora da shi safe da dare sati daya. 


*HANYA TA 7:-*

Masu matsalolin kogo/ciwon hakora da dafewar su ana samun lemon tsami rabi, danyar cittar da aka goge, gishiri kadan, a hade ana dangwala da brush ana goge hakora. 


*HANYA TA 8:-*

Masu matsalolin warin baki, amosanin baki, amosanin hakora datti da sauran su, sai a samu garin saiwar tumfafiya ana wanke baki sati daya.


*HANYA TA 9:-*

Ana amfani da garin alumun babban cokali 3 da garin yayan bagaruwa babban cokali 2 a hade su zama abu daya ana dangwala da yatsa ana wanke baki dan kore kowanne irin ciwon daya kama baki da hakora sati daya. 


*HANYA TA 10:-*

Ana wanke harshen daya kamu da baki/fari ko jan busa baba (kurajen dake fitowa a kan harshe masu zafin gaske) da rabin katon tomato 🍅 sai a dangwali gishiri da shi a wanke bayan ya kawo jini a barbada garin ararrabi me laushi a kwanta da dare kafin safiya ya mutu InshaAllah. 

SHARADIN AMFANI DA MAGUNGUNAN

Lallai ku sani magungunan da muka ambata suna da zafi dan haka a kula wajen wanke hakora kar suna yawan taba dadashi, kuma ayi daidai kwanakin da muka ambata kar a haura dan duk abun da zai haska hakora suna rage masa karfi koda wankin hakora na hospital ne yana da illa kar ya zama aikin ka kullum zarya hospital wanke hakora. 


By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻‍🍳

    {~07062950801~}




Post a Comment

0 Comments