Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

MACEN KWARAI ABIN ALFAHARIN MIJINTA AMMA SAIKIN KASANCE MAI WADANNAN HALAYYAN



 🥀 *_MACEN ƘWARAI ABIN ALFAHARIN MIJINTA_*🥀


" *Macen Ƙwarai* bata buƙatar malamai da ƴan Tsubbu domin mallake zuciyar mijinta, Ita har kullum Tamiƙa lamarinta ga ALLAH, Dakuma Sihrul halal,ma'ana kissa,  Biyayya haƙuri, Kawar da kai, Neman afuwar mijinta idan tamasa laifi, Yin abinda yakeso, da nisantar abinda bayaso.,"


"Bata ƙauracewa Shimfiɗar mijinta ko da kuwa yamata ba dai dai ba Domin tasan cewa wannan haƙƙi ne gareta Daya zamo wajibi ta sauke shi,"


"Bata Ƙullatar mijinta idan sun samu saɓani idan ya bayyana mata Yatuba takan karɓeshi hannu bibiyu Tamkar Komai bai faru ba"


Ita mai tausasa Harshe ce ga mijinta mai yi masa magana mai daɗi, Da Sake Fuska a garesa."


"Itace wacce annabi SAW yace idan ka kalleta Zaka ƙara samun nutsuwa idan ka kalle zakayi farin ciki, Kuma ko Rantsuwa kayi akanta bazakayi Kaffara ba,Saboda kasantuwarta ma'abociyar miji Tana komai ne domin tafarntawa mijinta rai, Kuma ta ɗauki Aure ibadar ALLAH bata Wasa da aurenta, mai godiya ce g abinda mijinta yke mata komai ƙanƙantarsa."


Madallah da macen Ƙwarai Alfaharin mijinta!!!


    Muyi kokarin munkyautatama junanmu dan musamu rabauta mudunga hakuri dajunan kodon aljannarmu tayi kyau.


By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻‍🍳






Post a Comment

0 Comments