wannan wani hadine na musamman wanda ake bukata amare suyi.ko masu niyyar aure.
Da farko sai asamu tatacciyar zuma mai kyau a aje gefe daya sai asamu :
DabiNo (ajuwa).
Garin hulba cokali 3.
Sai asamu man habbatus sauda dan misra maikyau sai garin ridi cokali 5.
Sai gyada itama cokali 5.
Sai a hadesu wuri daya su hadu.sai arinka sha cokali 3 safe da yamma.
Ko kuma a samu dabino (ajuwa)a hada da nonon rakumi da garin alkama cokali 4.sai a hadasu wuri daya a damasu a rinka sha sau daya arana da daddare.
Kokuma a hada kwa-kwa da dabino maikyau arinkaci sau daya arana.
bayan nan sai a hada madara da kankana mai kyau amman kankanar za'a jajjagata sai a hadata da madara a rinka sha safe da yamma.
Wacce ta rasa Budurcinta wato kamar bazawara ko kuma budurwa da akayiwa ( fyade ) ko kuma Wata hanya daban.
Mata da yawa suna aure cikin fargaba idan suka hadu da ( kaddara ta fyade KO kuma saduwa da namiji ) kuma hakan yayi sanadin rabuwarsu da budurcinsu don sun san maza da yawa sun fahimci hanyoyin da zasu gane mace idan ta rasa Budurcinta kuma Daga ( DAREN FARKO ) ango zai iya Fara canjawa amarya soyayyar sa harma wasu suna fadawa zuciyar su bazawara suka auro wato wani ya rigashi kwanciya da ita"_
Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da*
Ruwan dumi
Bagaruwa
Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki
GYARAN JIKI
ki sami ganyen magarya da lalle a dafa in Ya dan huce sai a shiga. in an fito Ayi tsumin DA kaninfari Na kwana uku sai ki nemi.
Garin hulba.
Habbatussauda
Alkama
Gyada
Ridi
danyar shinkafa
sai a hadesu a wuri guda a nike a dinga Yin kunu Ana sha DA nonon rakumi ko madara ko nonon shanu za’a sha DA awa biyu kafin Ayi bacci DA kuma awa biyu bayan anci abinci da safe
kuma idan xaki kwanta ki shafa man hulba a nonon naki wannan hadin in kinasha yana gyara Breast da fata.
yana Kara ni’ima ajiki sosai.
DOMIN MAGANCE BUSHEWAR GABAN KI
domin magance wannan matsala, Ana iya samun kwai daya, a buga Ya kadu sosai sai a sami ganyen ‘ugu’ a matse ruwansa, a samu ruwan ugun rabin kofi ki juye a kan ruwan kwanda ki ka fasa sai kuma ki saka zuma, cokali uku ki kuma kada wa sosai, ki zuba madarar gari cokali biyu kici gaba DA kada wa soaai sai ki Kara zuba lemun tsami bari daya don ki rage karnin ki kuma bugawa sai ki shanye idan kika yi kwana uku a jere duk bushewar gabanki sai ni’ima ta tsatsafo maki.
CIWON MARA KO CIWON CIKI.
idan mace tana ciwon mara ko ciwon ciki
a lokacin al’ada ko jinin yari kayi mata wasa
zuma cokali 5
man tafarnuwa cokali 2
in an hada sai ta rika sha cokali 1 DA safe 1 da yamma.
MATAR DA TAKE DA KURAJE A GABANTA
a gabanta ko take jin kaikayi a samu man tafarnuwa cikin karamin cokali sai ta matsa lemon tsami daya a cikin sannan ta rinka dan gwala da auguga tana shafawa a gabanta kwana 5 zata warke Insha ALLAH.
By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳
0 Comments