Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

WASU MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KISANARWA 'YARKI GAMEDA JIKINTA KAFIN TASHEKARA 10



Wasu Mahimman Abubuwan Da Yakamata Ki Sanarwa 'Yarki Game Da Jikinta Kamin Ta Shekara 10


Iyaye musamman mata sai su rika jin nauyi ko kunyar magana da 'ya'yansu mata game da sauyin yanayi jikinsu.

Wannan yasa yaran mata da dama kodai su fahimci abun a wajen wasu ko a Koyarwa na malamansu wanda hakan babban kuskure ne. Wannan yasa yara mata suke shiga tashin hankali a farkon ganin al'adarsu. Ko kuma idan sun soma tofo nonuwa sai kaga yarinya duk ta firgice.

 

Yanada kyau a matsayinki na uwa da zaran 'yar ki ta kai shekaru 10, ki soma nuna mata zata samu sauyin halitta daga jikinta.

Ki nuna mata nonuwanta zasu soma tsira idan ma basu fara ba. Nuna mata duwawunta suna iya kara girma idan mai irin wannan siffance.

Tabbatar mata da cewa zata soma al'ada idan lokacin yayi taga jini ya fito a gabanta, kada ta ji tsoro ta soma zama mace kenan. A nan ne za a tabbatar mata da cewa tana barin namiji ya taba hannunta zata yi ciki. Kuma idan tayi ciki wuta Allah zai shigar da ita. Sai idan tayi aure sannan zata yi ciki amma ba kamin aure ba.

A wannan lokacin ne uwa zata nunawa 'yarta yadda mace take zama kafafuwanta a rufe, yadda zata rika sunkuyawa idan zata dauki wani abu ko ajiyewa, da kuma yadda zata rika mu'amala da maza.

A dai-dai wannan shekarun ne uwa zata fahintar da diyarta mahimmancin tsaftace jikinta, tufanta da kuma muhallinta.


A wannan lokacin ne uwa zata koyawa yarta yadda zata rika yin mu'amala da zama cikin taka tsantsan nisantarsu.

Anan ne yakamata ta fahimci darajar da jikinta yake dashi domin ta rika saka sutura masu kyau.


A shekarun ne uwa zata nunawa 'yarta irin abinci da yake dacewa da mace da wanda ba cimar mace bane.

 

Abu mafi mahimmanci game da illimintar da diya mace a wannan shekarun shine cusa mata tsoron Allah.

Nuna mata irin darajar da mace take dashi idan ta kare mutuncinta ga maza mabarnata. Cusa mata karfin hali da rashin tsoro na marin duk namijin daya nemi ya tabamata nonuwa ko jikinta.

Allah Ya shiryer damu da abunda muka haifa dama masu zuwa da bamu haifa ba.






Post a Comment

0 Comments