Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKI KIYAYE NONONKI LOKACIN DA KIKE SHAYARWA WATO (BREAST FEEDING)



 *YADDA ZAKI KIYAYE NONONKI LOKACIN DA KIKE SHAYARWA*


Nonon mace dayafi kowanne kyau shine ake ƙira (Fundamental straight ) yana jure wahala bayan shayarwa da yawa yana kasancewa a tsaye da taurinsa 

Amma duka haka idan ya haɗu da rashin kula lokacin shayarwa zai iya lalacewa, 


domin kula da gyaruwar nononki daga haifuwarki ta fari ki tabbatar kina taka tsantsan yanda Zaki gama shayarwa kiyi gyaran nononki ya dawo kamar kina budurwa, wannan shine martaba ta mace abunda zai ƙara miki daraja a wajen miji,


Abu na farko shine ba'a manna bakin yaro akan neple yanda bazaisha iskaba haka zakila ba'a shayarda yaro nono yana zuba ki kiyaye da wannan,


Ba'ayin bacci ana shayarda yaro, gaba ɗaya ma ba'aso ana shayarda yaro a kwance yanda Zaki kwanta akan ɗaya nono kuma kina bashi ɗaya, sannan Yara da suke daɗewa sunasha ana canja musu nono kada ya zama tsawon lokaci yana Shan ɗaya domin haka nasa nono ɗaya yafi ɗaya, kuma neple ɗin bazaisha iskaba,


Ba'ayin jima'i ana shayarda yaro nono sannan ba'a kwantarda yaro abashi nono ta sama wato kiyi rubda ciki a kansa,


Ba'a barin yaro yasha nonon wata daban sannan ya dawo Shan na mahaifiyarsa, Hakan yana banbanta tsosan Wanda Hakan zai kawo yamushewar neple, Wanda sanadiyar haka nono ya kasa gyaruwa, Hakan tasa wasu na ganin idan mace na shayarwa to kada ta bari mijinta yana tsotsa yanda yaron yake, ya samu wani salo na daban Wanda tsotsansa bazai rinka zuboda ruwan nono ba,

Sannan kuma Hakan baya Hana kiyi abinda ake cewa (multiple  peeding) wato idan kina shayarda yaronki ki hada da wani yaron, abunda dai ba'aso yasha nonon wata kuma kema yana Shan naki,


Ba'a barin farin nono dake zuwa ya gushe kafin a fara shan maganin yaye, da zaran lokacin yaye ya kusa idan kika fuskanci ruwan nonon ya fara komawa kamar ruwan famfo to kiyi maza ki fara domin idan wannan farin ya gushe kafin nono ya dawo ana shan wahala.  


By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻‍🍳



Post a Comment

0 Comments