*YADDA ZA KU KULA DA JIKINKU A LOKACIN SANYI*
Fatar jiki ita ta fi komai girma a jikin mutum, sannan ita ce ke fara bayyana da an hango mutum. A lokacin sanyi takan bushe ta yi fururu, musamman dai idan ba a kula da ita yadda ya kamata.
*Akwai hanyoyin kula da fata sosai da suka haɗa da:-*
*Kar a yi wanka da ruwa mai tsananin zafi:-*
Haƙiƙa an san cewa yin wanka da ruwan sanyi ba abu ne mai yiwuwa ba ga mafi yawan mutane a lokacin hunturu, sai dai kuma shi kansa yin wanka da ruwa mai zafi sosai ba zai taimaka ba a wannan yanayi don zafinsa na iya yin tasiri sosai a kan fatar.
An fi so a yi wanka da ruwa mai ɗumi kawai a yadda bai yi sanyi da zai sa kaɗuwa ba, sannan bai yi tsananin zafin da zai kashe fatar ba. Ruwan zafi sosai na kashe fatar jiki.
*Yawan shafa mai:-*
A irin wannan yanayi an so da zarar mutum ya gama wanka tun kafin ya tsane to ya shafa mai a illahirin jikinsa tun daga banɗaki. Sannan ana so cikin mayukan ya kasance akwai mai ɗan ruwa-ruwa da ake kira lotion sai a cakuɗa da mai maiƙo a shafe a jikin.
*Mayuka:-*
irin su man kaɗanya da man kwakwa da zaitun na matuƙar taimakawa a irin wannan yanayi.
*A dinga shan ruwa sosai:-*
Mutane da dama suna tunanin kamar a lokacin zafi ne kawai aka fi buƙatar shan ruwa sosai. Sai dai masana lafiya sun ce a lokacin sanyi ma ana so a yawaita shan ruwa saboda yana taimakawa wajen ƙara ingancin fatar jiki da hana ta bushewa.
*Cin ganyayyaki da ƴaƴan itace::-*
Sannan Maryam Muhammad ta ba da shawarar yawan cin abincin da ya danganci ganyayyaki da kayan marmari kamar su dankalin Hausa da karas da gurgi da lemo da sauran su.
*Hanya ta gargajiya:-*
Akwai wasu dabaru da za ku iya bi don inganta kyawun fatar jikinku. Daga ciki akwai yin Halawa da dilka, wani salo da ya samo asali daga Larabawan Sudan da ƴan Chadi.
Ana dafa sikari ne sosai a zuba wasu sinadarai sai a dinga sawa a jikin mutum ana cire gashi da duk dattin da ya maƙale a fatar. Sannan a mulke jikin da sinadarin dilka ɗin a yi ta bi ana murzawa na wani ɗan lokaci.
Sannan akwai turara jiki ta hanyar zuba ruwan zafi a bokiti sai a lullube jiki tare da bokitin don jikin ya turara. Amma a kula kar a bari ruwan ya zube ya ƙona ku,
*Ƙafafu*
Ƙafa wata muhimmiyar ɓangare ce ta jiki da take buƙatar a dinga kula da ita sosai, musamman a lokuta irin sanyi.
A dinga haɗa ruwan ɗumi ba mai zafi sosai ba sai a zuba ruwan kal wato vinegar kaɗan da ɗan gishiri, a tsoma ƙafa a ciki ta yi kamar minti 30 ko zuwa lokacin da ruwan zai huce, sannan sai a wanke ta tas da dutse goge ƙafa, ko kuma abin goge ƙafa na zamani.
A dinga wanke ƙafar akai-akai ana kuma shafe ta da mai musamman ma na kaɗanya da zarar an gama wanke ta.
A kuma dinga saka safa sosai a ƙafar don kaucewa kwasar ƙura ko datti ta yadda za su haifar da faso ko kaushi. Sannan a tabbatar ko a gida ne ana yawo da takalmi.
*Gashi:-*
Shi ma gashi kamar yadda aka sani ya fi buƙatar kulawa sosai lokacin sanyi.
Don haka ƙwararrun suka ce:-
A dinga yawan shafa masa mai da kuma rufe shi idan da hali a dinga zama da kitso maimakon barin sa a tsefe a dinga shan ruwa sosai don yana kare gashi daga karyewa idan da hali a dinga yin abin da ake kira steaming, wato turara gashin makar bayan duk mako biyu.
*Leɓe*
Shi ma leɓe muhimmin waje ne da ke son kulawa ta musamman a lokacin sanyi. Jawahir ta ce yana da kyau a dinga yawan shafa man baki a leɓen saboda gudun bushewarsa.
Idan leɓe ya bushe a lokacin sanyi har wani daddarewa za aga yana yin jini. Sannan ya kamata kuma a dinga shafa masa man baki da daddare idan za a kwanta barci
0 Comments