A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN
1. ki tsayar da saurayi guda daya tak na kirki bisa la
akarai da ayyukan sa da halayensa na zahiri.
2. kitabbata kina sonsa sosai kuma shima yana sonki sosai.
3. Kada ki yarda kidade da saurayi, ko kishaqu dashi
ko ki nuna masa tsananin so batare da iyayensa sun
gana da iyayenki ba. In yaqi turosu kirabu dashi
tunkafin yagama sace zuciyarki.
4. Kizama mebin shawarar iyayenki, da neman
shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar
Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.
5. Kada kiyarda a kawo miki gulmar saurayinki ke
kuma kidauka koki kama zargin sa. A'a sai kinyi
bincike na adalci ko kingani da idonki.
6. Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki qarya kizama me
fada masa gaskiya, da yimasa bayanin komai iya
saninki.
7. Kizama me yawaita addu'ah da bawa Allah zabi a
dukkan lamarinki.
8. kikiyaye zargi da binciken laifinsa matuqar ya sanar
dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.
9. kidauka dan adam tara yake bai cika goma ba,
kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa afuwa.
10. kizama me kare mutuncin kanki, da kuma kulada
matsayinki batare da girman kaiba ko jan aji ga
masoyi... JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE
HAIFARWA SAI NADAMA. idan saurayinki ya tsaneki
ko yagudu yabarki ko kin rasa wani abu da yake baki,
kiyi haquri kada kijuya masa baya, kisa masa shakka
a ransa yadinga tunanin anya kuwa kina son sa da
gaske???
*YAU TSARABAR TAWA GA ZAFAFAN YA,N MATA NE NA WANNAN GIDA🥳
KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA TAKUNKI EHE 😎
🥳 Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki
fuska
yana shigo miki da kalmomin da basu
daceba ko
dabi'u.
kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar
waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga
fulawarki ,ko
zai auna kaurinki dadai sauransu.
SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI
ADUK
SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI
KIRABU
DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE
YA
BATAKI.
Wakilin shaytanne.
🥳 Kizama me yiwa saurayinki Al-qawarin
nuna
masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi
masa
biyayya dai dai gwargwadon
iyawarki.
Akuma kiyaye yaudara da cin amanar juna.
0 Comments