Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ABUBUWA (60) DASUKE KAWO MUTUWAR AURE WANDA DUK WASU MA'AURATA AKESON SU KIYAYE SU


 ABUBUWA (60) DA SUKE KAWO MUTUWAR AURE


Rayuwar Aure an gina ta ne kan Nutsuwa da Soyayya da tausayi, tsakanin miji da matarsa   tare da fahimtar juna da mutuntawa da kyakkyawan zama a haka ne miji da mata zasu yi rayuwa mai tsawo,  ba tare da wani ya shiga hakkin wani ba. 

Wannan yasa shaidan yake kai kawo da zirga zirga da kulle-kulle da kutungyila wajen lalata harkar Aure, 

Sabo yasan in Aure ya lalace  komai zai iya lalacewa sakamakon lalacewarshi, wannan yasa Malamai da masu bada Tarbiyya da kuma masu lura da al'amuran al-umma suke kara wayarwa da alumma kai, akan sake-saken Aure da kuma hadarinsa sakamakon yakan haifar da rugujewar gida, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tsaro da rashin zaman lafiyar al-umma, don haka mukayi nazari bayan bincike da tattaunawa, da  wadanda suka shiga irin wadannan matsaloli, da bibiyar dalilan da suka jawo hakan, musamman lokacin shirin auren Zawarawa da muka gabatar ƙarƙashin gwabnatin jahohi 

Dan haka muka fitar da Dalilai guda  dari (60 ) wadanda muke gani sune ummul aba isin wadannan matsaloli wadanda idan ba a kula da suba za a samu mutuwar aure. 

mun kasa wadannan matsaloli zuwa kasha uku (3) : 

1. Matsalolin da suke faruwa kafin Aure 

2. matsalolin da suke faruwa lokacin Aure 

3. matsalolin da suke faruwa bayan Aure 

Wadannan matsalolin guda uku a kwai masu zuwa daga ɓangaren mata akwai, akwai masu zuwa daga ɓangaren maza a kwai, akwai masu zuwa daga duka bangarorin guda guda biyu :

Don haka cibiyar mu ta LOVE AND MERCY SCHOOL FOR MARRIAGE COUNSELING

ta ɗauki waɗannan abubuwa ɗaya bayan ɗaya take shirya bitoci akai. 

 

1. Al-Adu   

2. Rashin Ilimin Zamantakewar Aure 

3. Rashin Zabin Matar Kirki Ta Gari 

4. Auren  Babu Soyayya Daga Miji Ko Mata 

5. Gaggawar Yin Aure Batare Da Mutum Ya Shirya Ba 

6. Banbancin Ilimi 

7. Rashin Binciken Halin Miji Kafin Aure 

8. Rashin Binciken Halin Mata Kafin Aure 

9. Matsalar Iyayen Miji 

10. Matsalar Iyayen Mata 

11. Matsalar Dangin Miji 

12. Matsalar Dangin Mace 

13. Rashin Tsafta 

14. Rashin Iya Kwalliya 

15. Rashin Iya Magana 

16. Rashin Ciyarwa 

17. Rashin Iya Kwanciyar Aure 

18. Rashin Adalci 

19. Goyon Kaka (Yar Shagwaba) 

20. Auren Kisa Wuta 

21. Zaman Gidan Haya 

22. Ruwan Ido Wajen Neman Aure 

23. Auren Bariki 

24. Auren Mace Don Kudinta 

25. Auren Dole 

26. Matsalar Talauci 

27. Matsalar Qawaye 

28. Zafin Kishi 

29. Rashin Haihuwa 

30. Rashin Ladabi 

31. Rashin Kunya 

32. Shaye-Shayen Kayan Maye 

33. Qannen Miji  

34. Qannen Amarya 

35. Abokan Miji 

36. Sata 

37. Gulma 

38. Tsananin Damuwa 

39. Rashi Lafiyar Mace Wajen Gamsar Da Miji 

40. Rashin Lafiyar Miji Wajen Gamsar Da Matarshi 

41. Sharrin Bokaye 

42. Rashin Shawara Tsakanin Miji Da Mata 

43. Aikin Mace (Ta Zama Yar Kasuwa Ko Ma’aikaciya) 

44. Rashin Ilimi Da Samun Wayewa Akan Aure 

45. Rashin Daukar Nauyin Iyali Wajen Basu Haqqi 

46. Cin Bashi Ayi Aure 

47. Yawan Tafiye-Tafiye (Bala Guro) 

48. Yawan Zuwa Unguwa 

49. Cin Amanar Aure Daga Miji Ko Mata 

50. Shigar Da Qawaye Ko Abokai Cikin Harkar Iyali 

51. Rashin Kula Da Addini 

52. Girman Kan xaya Daga Cikin Ma’aurata 

53. Rashin xaukar Aure A Matsayin Ibada 

54. Butulci Da Manta Alheri 

55. Samun Larura Ko Wani Ciwo Mai Tsanani 

56. Yawan Shigar Iyaye Cikin Harkar Aure 

57. Al’mubazzaranci 

58. Rashin Godiya  

60. Mummunan Zato 

61. Rashin Nuna Tausayi Da Damuwa Da Juna.

Allah ya daidaita tsakanin ma'aurata. Ya bada zaman lafiyar a aure...



Post a Comment

0 Comments