Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

BANBANCIN TSAKANIN SHA'AWA DAKUMA SOYAYYA


BAMBANCIN DAKE TSAKANIN SHA'AWA DA KUMA SOYAYYA // 21

Maganar kallon wace za ka nema, ko ita ta san wanda zai aure ta abu ne mai matuqar mahimmanci, Annabi SAW ma ya kwadaitar a kan haka, kenan wannan ba wata matsala ba ce, to amma me ya sa wasu 'yammatan ba sa sanin wadan da za su aura sai dab da daura auren? Wani dalili ne yake sa 'yammata suke zuw ga saurayi da niqabi a ranar farko, bayan bangajejen hijabin da ya sauka har qasa ga safar hannu da ta qafa? Wai gaskiya ne saurayi yana da damar kallon ko'ina a jikin budurwa kafin ya fara nemanta? Ya zancen shi saurayin, shi ma sai ta ga ko'ina a jikinsa kafin ta amince da soyayyarsa? Wadannan mas'alolin nake so mu dan bincika su gwargwadon fahimta.

.

To da yake aure al'amari ne mai matuqar mahimmanci, wanda yake da alaqa ta kai tsaye da dangantaka, ciyarwa, gado da wasu abubuwa da suka shafi rayuwar aure, kamar dai jin dadin wasa da juna, kallo da saduwa, ya zama dole kenan a tantance kafin a shaqu, in da a ce auren holewa wane, ba wata matsala, saduwa ce kawai kamar yadda sauran dabbobi suke yi in sha'awarsu ta motsa, sannan abin da ake nema kowace mace tana da shi, kuma iri daya ne, kowa ma sai mutum ya dauka in ya gama biyan buqatarsa ta wuce, ba wata matsala tunda zina ce, aure sam ba haka yake ba.

.

Na taba yin wani aboki da ya riqa kwasan wata yarinya, sun yi shekaru yana mu'amalla da ita, sai na yi niyyar sauya masa tunani da cewa, da ya aure ta kawai, don auren yana da fa'idoji da yawa:

1) Zai hana ta yin zina da kowa, za ta komo ta zama saliha, yana da lada.

2) Zai daina samun zunubin zina ya koma samun ladar saduwa.

3) Za ta fara samar da diyoyin da muslunci zai yi alfahari da su.

4) Za a daina yi masa kallon mazinaci kuma mutumin banza.

.

Sai gogan na ka ya ce shi sam ba zai iya mai da mazinaciya uwar 'ya'yansa ba, na dai gaza yin haquri na ce "To ba da kai take yi ba, da wa take yi?" Ya kafe kan cewa shi tsarkakakkiyar yarinya yake so ba wace yara suka hole da ita ba, -ikon Allah- idan tunanin kowa ya zama neman tsarkakakkiyar yarinya wace za ta zama lafiyayyen irin da zai ba da yabanya mai kyau, to ya zama dole a tantance abubuwa da dama, lafiyarta, kyawun da ya bayyana da wanda ya boyu, da dai sauran abubuwan da suka kamata.

.

Kuma ya zama dole kowanne cikin ma'aurata ya san komai dangane da wanda zai aura tun kafin a kai ga daura auren, shi namijin ya yi bincike game da ita da irin tarbiyar da ta samu, ita ma kafin ta amsa masa ta tambayi uwayenta, masamman mahaifinta kamin a je ga shaquwa, uwayen za su san sa, su san halayyansa ta wurin abokansa da maqwabtansa, da ma wadan da yake mu'amalla da su, ta nan ba a yi wa aure shigar burtu ba kenan, rayuwa ce ta dindindin mai ci gaba har lokacin da dayansu zai koma ga mahalicci ko su dukansu biyun.

.

Galibi hanyoyin da muke bi wajen zaben mace sun taqaita ne ga kyawun sura, in dai ita fara ce kyakkyawa shi kenan ta yi, wani abin da ya shafi mutunci da kyawun dabi'a kuma sai daga baya a bincika, sau da yawa binciken ma bai da wani amfani, tun da ba wani abin da za a canja, wannan dalilin ne ma ya sa macen da ta fito baqa sai ta nemi canja launi ko za ta sami shiga, su ma matan sukan dauki sulalla a matsayin hanyoyin yarda da saurayi, shi ma sai ya fara qoqarin gamsar da ita da qarairayi daban-daban na kudi, sutura, sana'a da hurdodi kala-kala ko za ta amince, ba a neman aure da yaudara, akwai buqatar tantancewa.

.

Wannan ya sa Shari'a take ganin wajibcin tantance 'yammata da samari, ta yadda in mutum yana son aure dole ya neme ta daga hannun uwayenta, in kuma ya qi zuwa to ba ya son a tantance shi ne, bai kamata budurwa ta yarda ta fara hira da saurayi ba har sai ta jira sakamako daga mahaifinta, akwai abubuwa da dama da mahaifin zai duba cikinsu harda aqida, al'ada, dabi'a, ilimi, lafiya da mu'amalla, ita yarinya abu daya kawai take dubawa, ko dai ya yi ma ta ko bai yi ba, irin wannan wautar da 'yammata suke yi na kwashe-kwashe ne yake sa wa wata take auren wanda zai tilasta ta tafiya daga Kano har Kaduna a qasa, in kika ji ya ce ba zai iya zuwa wurin babanki ba to ki ja layi.





Post a Comment

0 Comments