Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

BAYANAI GAME DA CIWON SANYIN MATA (VAGINAL INFECTION) TARE DA MAGUNGUNA



 Bayanai game da ciwon sanyin mata (Vaginal infection):


Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'.


Mene ne ciwon sanyi mata?


Ciwon sanyi ko toilet infection ko vaginal infection duka na nuni akan abu daya ne. Ciwon sanyi wasu kwayoyin cuta ne da ke addabar al’aurar mace har ma da maza .Wannan kwayoyin cutar na hana sukuni ta hanyar janyo kaikayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa fari, ko doruwa ko kore, ko jin zafi yayin jima'i, jin zafi yayin fitsari da sauransu.


Wannan fitar ruwan yana iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ko rashin lafiya ba. Mata sun fi yawan samun kansu a wannan yanayi na fitar ruwa daga mafitsararsu fiye da maza. Saboda haka a wannan bayanin da zanyi, zan fi karkata a kan mata.


Yanayin yadda Allah (SWT) ya yi cikin al’aurar mace shi ne, ya kasance a jike (mai danshi-danshi) a ko wane lokaci. Ruwan da ya ke jika gaban mace yana fitawo ne daga wasu bangarori daban-daban da suke cikin gaban nata. Yawan ruwa yana iya karuwa, ko raguwa ko kuma ya dauke gaba daya. Wannan zubar ruwa ana kiransa “vaginal discharge” a likitance. Hausawa suna kiransa da “ciwon sanyi”, wasu kuma suna kiransa da “toilet infection (ma’ana, cutar da ake dauka a bandaki maras tsafta)”. Ya kamata a sani cewa, har yanzu, a likitance, ba’a tabbatar da cewa yin amfani da bandaki maras tsafta yana daya daga cikin hanyar da ake kamuwa da wannan cutar zubar da ruwan ba, amma dai ana zargin hakan, kuma ya kamata a yawaita tsaftace banɗaki.


Me ya ke janyo yawan zubar da ruwan?


Kamar yadda na fada a baya, shi yawan zubar da ruwan zai iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ba.


Abubuwan da suke janyo zubar da ruwa ba na cuta ba


Juna biyu (ciki): Amma fa wani lokacin, juna biyu yana iya janyo zubar ruwa na cuta.


Yin amfani da kwayoyin tsarin iyali

Lokacin jinin al’ada.


Abubuwan da suke janyo zubar ruwa na cuta


Shan magunguna barkatai, musamman waɗan da ake kira da antibiotics ko steroid da sauran su.


Cututtuka a jiki kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu.


Juna biyu (ciki): yana iya janyo zubar ruwa na rashin lafiya da kuma wanda ba na rashin lafiya ba.


Saduwa da wanda ya ke dauke da cutar: namiji zai iya dauka daga wurin mace, sannan mace ma zata iya dauka daga wurin namiji.

Zinace zinace.


Yawan wanke cikin gaba da wani sinadari (vaginal douching).


Masan tangaran (toilet seats): Musamman idan wadda take dauke da cutar ta yi amfani da shi kuma bata wanke masan ba. Amma fa har yanzu ba’a tabbatar da wannan hanyar ba


 Alamunta, hanyoyin kamuwa da kariya daga gare ta


Idan mace tana da, ko kuma, tana aikata daya daga cikin wadannan abubuwan, to zata iya kamuwa da wannan cuta ta zubar da ruwa.


Ire-iren ciwon sanyi


Ciwon sanyin da ke damun mata bincike ya nuna kala kala ne. Amma zamu takaita akan guda 3 wanda sune suka fi cutar da mata.


Wanda bacteriya ta ke janyowa (Bacterial vaginosis).


Wanda fungi ke janyowa (Yeast Infection ko Candidiasis).


Wanda ake kamuwa ta hanyar jima'i

Wanda bacteriya ta ke janyowa (Bacterial vaginosis)


Wannan yana daya daga cikin manya manyan da ke janyo wannan cutar. A cikin mata 100 da suke da ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vaginosis ne. Wannan na faruwa ne saboda yanayin canji na bacteriya ɗin da ke jikin mace.


 Asali akwai bacteriya masu bada kariya a gaban mace wanda ake kira da "normal flora". Idan wannan bacteriya suka habaka suka yadu sukan zama ƙwayoyin cuta kaman 'Gardnerella vaginalis' sai su haifar da ciwon sanyi.


Maganin bacterial vaginosis (Wannan misali ne kawai dole sai mutum ya ga likita kafin ya sha ko wani irin magani)


Wannan kalan ciwon sanyin na faruwa ne sakamakon girman kwayoyin cutar 'fungus' wato Candida albicans a cikin al'aurar mace. Asali gaban mace na dauke da wannan ƙwayoyin halittar amma basa cutarwa har sai sun kara yawa. Suna kara yawa ne idan suka samu damshi, ko waje marar iska.


Wannan kwayoyin cutar ba farji kadai suke tsayawa ba suna iya yaduwa a cikin jikin mutum.


 Mata da yawa suna kamuwa da wannan cutar a wani lokaci a rayuwarsu. A cikin kashi 100 kashi 75 sun kamu da shi. Cuta ce mai hatsarin gaske idan ba a maganceta da wuri ba musamman ga masu ciki, ko masu ciwon suga ko kuma masu dauke da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV.


Amma ciwon sanyi na yeast, ba ciwon da namiji sai iya dauka ba ne, bayan jima'i duk da cewa bincike ya nuna a cikin kashi 15 cikin 100 na maza na samun kaikayin gaba ko fesowar kuraje bayan saduwa da macen da ke dauke da wannan cutar.


Alamun yeast infection


Kaikayin gaba.

Radadi a farji

Fitan farin ruwa mai kauri, ko mai yanayi kamar awara.

Jin zafi yayin jima'i

Labben farji suyi jawur ko su kwaile

Fesowar kuraje.

Maganin yeast infection (Wannan misali ne kawai dole sai mutum ya ga likita kafin ya sha ko wani irin magani)


Akwai magungunan da za ki sha domin magance wannan cutar.


Fluconazole (Diflucan) ko

Itraconazole (Sporanox)

Likita zai miki bayanin akan yanda za ki sha magungunan.


Sannan idan cutar bata fara karfi ba akwai wasu magungunan da za ki yi amfani da su. Wannan sakawa a ke yi a cikin farji, akwai vaginal tablets ko creams na kwana 7 zuwa 14 da ya danganta da yanda likita ya ce ki yi amfani da shi. Koda kin fara amfani da shi sai ki ka ji sauki bayan kwana 2 ko 3 kada ki daina amfani da shi ki ci gaba har sai kin gama dose din saboda idan cutar bata mutu ba za ta iya dawowa. Daga ciki akwai;


Nistatin (Mycostatin)

Miconazole

Clotrimazole ( wannan yafi karfi a cikinsu).

Yana da kyau idan ana maganin ciwon sanyi a canza wanduna, idan kuma babu hali a wanke su dukka da ruwan dumi a shanya a rana.


Wanda ake kamuwa ta hanyar jima'i


Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa da shi ne ta hanyar jima'i wato mata za ta iya shafawa mijinta idan tana mu'amala da wasu mazan. Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yana da mata sama da daya ko kuma idan yana neman mata.


Namiji ba kasaifai ya ke ganewa yana da wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayyana a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana a jikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana da shi.


Amma idan anyi sa'a ya bayyana a jikin namiji akwai alamomi kaman haka:


Jin zafi wajen fitsari

Jin zafi bayan fitan maniyyi

Fitan farin ruwa kadan

Kaikayin gaba

Alamomin na mata


Kyaikayin gaba

Jin zafi wajen fitsari

Warin gaba

Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tas.

Kwailewar farji

Yadda za ki magance wannan cutar shine amfani da wannan magani mai suna Metronidazole.


Mata da maza duka za su iya amfani da wannan maganin matukar suna dauke da cutar, kuma za su kauracewa saduwa har sai sun warke.


Wasu alamomin ciwon sanyi


Ciwon mara: Ciwon sanyi na janyo ciwon mara sosai koda ba lokacin ala'ada ba.

Wasa da al'ada: Sai ki ga ala'adarki na miki wasa, ko yanayin fitar jini ya karu.

Dabi'unmu na yau da kullum da za su iya janyo wannan cutar na ciwon sanyi da rigakafinsu.


1. Yanayin tsaftace farji


Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shine dai dai. Kaman amfani da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami, medicated soaps da sauransu. Wanann ba tsaftacewa za suyi ba, hasalima kina kara bata halittar farjin. Kaman yadda muka yi bayani a baya game da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjin. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa.


2. Yanayin wanke dubura bayan an yi bayan gida


Asalin yadda ya dace a wanke bayan gida shine farawa daga gaba zuwa baya, ma'ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka sukeyi. Wannan dabi'ar sam bata dace ba. Idan aka fara daga baya ana debo ƙwayoyin cutar da ke cikin bayan gida ana aikawa cikin farjin. Hakan zai janyo da matsala babba. Shi farji baya san bakon abu a tattare dashi.


3. Amfani da bandaki mai datti


Yawancin mata na ɗaukan ciwon sanyi bayan amfani da bandakunan da mutane da yawa ke amfani wato public toilet. Shi yasa ake cewa ciwon sanyi toilet infection.


Mutane na da wata dabi'ar sayan magani barkatai ba tare da sanin likita ba. Misali yawan shan antibiotics da an ga kurji a jiki ko ciwon wuya da sauransu, na janyo infection. Bama vaginal infection kawai ba, hadda wasu cuttukan ma na daban. Saboda haka a kiyaye yawan shan antibiotics batare da sanin likita ba.


Idan mace na tsarin iyali domin samun tazarar haihuwa to akwai tabbas din da zata iya kamuwa da ciwon sanyi. Saboda yanayin chanji na kwayoyin hallitarta (hormones) na shafar farjin mace. Koda ana shan pills, ko implant a hannu, ko an daure bakin mahaifa da dai sauransu.


Hanyoyin kariya daga kamuwa daga wannan cuta


A daina amfani da magunguna barkatai ba tare da shawarar likita ba, musamman wadan da ake kira da antibiotics da kuma steroid.

A kauracewa zinace zinace.

A daina tura ko kuma zura wani abu a cikin gaba (al’aura)

Wadda take da cutar, ta je ta nemi magani a asibiti saboda kada ta shafawa wani ko wata.

Kammalawa


Zubar ruwa daga gaban mace yana damun mata kwarai da gaske, amma ba kowanne bane ya ke na cuta ba. Idan na cutar ne kuma, ana iya warkewa idan an sha magani. Kuma har yanzu, a likitance, ba’a tabbatar da cewa ana daukar cutar a bandaki ba. Allah ya kara mana lafiya da zama lafiya da ilimi mai amfani. Allah shi ne mafi sani, Y-a kuma bamu dacewa duniya da lahira. Amin





Post a Comment

0 Comments