Maza da dama na kokawa ko mamakin yadda mata suke iya rokon samarinsu kudi. Wasu mazan na mamakin haka, wasu kuwa suna ganin ba wata matsala bace idan har budurwar da namiji yake soyayya da ita ta nemi kudi a wajensu.
Akwai wasu dalilan dake sa mata suke rokon samarinsu kudi kamar haka.
1: Hakan Ya Dace: Bisa dabi'a ko al'ada dama addini, maza ne suke daukar nauyin mata. Wannan yasa duk wata mace datake soyayya danamiji sai ta rika ganin cewa shi wannan masoyin nata shi ya kamata ta tambaya.
Wannan yasa mata suke rokon samarinsu kudi.
2: Ganin Wadatar Namiji: Wasu matan muddin suka fahimci wanda suke soyayya dashi yanada abun hannunsa, wannan macen bata jin nauyin rokonsa kudi.
3: Kora Da Hali: Wasu matan hanyar mafi sauki da suke bi su kori namijin shine su nemi kudi masu yawa ko akai akai a gunsu.
Irin wadannan matan da zaran sun samu wata dama zasu ce maka ana binsu bashi ka biya musu, ko ta daura maka nauyin kawayenta ko 'yan uwanta. Da zaran ka kasa sai hakan ya zama hujjar da zata rabu da kai da manufar baka kulata.
4: Yawan Buri: Akwai matan da burinsu ko bukatunsu yafi karfinsu, don haka a kullum suna cikin rokon samarinsu kudi.
Irin wadannan matan, duk sati ba a rabasu da dinkin buki, tafiye tafiye. Ko son sayen wani abunda yafi karfinta.
5: Talauci: Wasu matan dole ce kawai yasa suke rokon samarinsu kudi amma ba domin suna so ba.
Irin wadannan 'yan matan idan basu roki samarinsu kudin ba suna iya zama ko kwana da yinwu. Wata ma kudin da zata sayi kunzugun al'adar ta Bata dashi har sai ta roka.
6: Zina: Idan mace ta fahimci masoyinta ya uzura mata da ci, ita kuma sai ta yawaita rokon kudi a wajensa domin gudun tayi biyu babu. Bai aureta ba bata kuma amfana da arzikin sa ba.
7: Tabbatar Da Namiji: Mata sukan roki samarinsu kudi ne domin fahimtar ko zasu iya
dasu bayan auren.
Irin wadannan matan da zaran sun fahimci masoyinsu mutum ne da ba zai iya yi mata hidima ba, daga nan take sallamansa.
8: Rainin Wayo: Akwai matan da suke rokon samarinsu kudi ne saboda sun rainawa samarin nasu wayo.
Idan mace ta fahimci son da namijin yake mata ya wuce misali zai iya mata komai idan yana dashi, idan ma Babu sai ya nemo, da zaran mace ta fahimci haka zata maida shi ATM.
9: Tabbatar Da Soyayya: Wasu matan suna rokon kudi wajen manemansu ne saboda kauna da soyayyar da suke yiwa namiji suke son ganin ya basu kudi sun sayo wani abun ko ya musu kyautan wani abun.
Irin wadannan matan da zaran mai sonta ya mata hakan dadi suke ji kuma hakan zai sa suyi ta yayatawa shine ya bata kudi tayi abu kaza, ko ya sayo mata wani abun.
10: Kishi: Musamman matan da suke soyayya da namiji mai mata.
Idan tana soyayya da namiji mai mata zata rika yawan rokonsa kudi ne a matsayin yana yiwa matarsa ta gida hidima ita kuwa sai oho. Don haka sai ta rika kirkiro matsalolin da mai sonta zai rika fitar da kudi yana bata.
Kowace mace da irin nata dalilin dayasa take rokon kudi a wajen mai sonta. Wasu matan ma rashin wayo ne ko gogewa na rayuwa suke rokon samarinsu kudi. Ko saboda karancin shekaru na rashin sanin illar yin hakan ko kuma batayi gogewan da zata fahimci hakan bai dace ba.
0 Comments