DUK FUSHIN DA ZAKI YI DA MIJIN KI KADA KI SAKE KIYI MASA WADANNAN ABUBUWAN
Akwai matan da suke wuce gona da iri a lokacinda suka samu matsala da mazansu.
Dole ne a rika samun matsaloli a tsakanin ma'aurata, amma duk irin matsalar da zaki samu da mijinki kada ki kuskura ki masa wadannan halayen.
1: Duk irin matsalar da zakuyi da mijinki kada ki shigo da raini a tsakaninku.
Ki ci gaba da masa biyayya koda kina fushi dashi. Amma shigowa da raini ko kaskantashi saboda kun samu matsala ba naki bane.
2: Duk irin sabinin da zaki samu da mijinki kada ki daina abubuwan da kikasan kina masa wadanda yake so.
Idan duk safiya kece ke zaba masa kayan da zai sa, kada ki fasa masa hakan saboda kina fushi dashi.
3: Duk bacin rai kada ki daina dafawa mijinki abinci.
Ko da kece kike taimakon gidan da kudin abinci kada ki fasa saboda kun samu matsala.
4; Akwai matan da idan suna fushi da maigidan sai ya shafi 'ya'yansu. Kada ki cutar da yaranki kona abokiyar zamanki saboda mijinki ya bata miki rai.
5: Duk tsananin masifan da zaku yi da mijinki idan ya bukaceki mika masa.
Wasu matan idan suna fushi da mazansu sai suki yarda suyi kwanciyar aure dasu. Wannan ba hanya bace da zaki warware matsalarku.
Da fatan mata zasu kiyaye wadannan abubuwan domin samar da ingantancen Zamantakewar aure.
0 Comments