Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

HAƊIN TURAREN TSUGUNO NA MATAN AURE KIRABU DA INFECTION KI MATSE


YADDA AKEYIN HADADDEN HADIN TURAREN TSUGUNO NA MATAN AURE NA MUSAMMMAN DON GYARAN GABAN MACE KIRABU DA INFECTION KI MATSE


 Turaren tsuguno, turare ne na ma'aurata da zakuyi amfani dashi donyin matsi gareku. Kuma wannan turare da zakiyi zai kara muki Dan-dano wanda da zarar mai gida ya sadu dake to zaiji matukar canji a gareki sannan kuma ke kanki saikinfi jin dadin saduwar wannan rana. 


Batare da bata lokaci ba zamuyi bayanin hanyoyin da zakubi wajen samuwar wannan turare, abubuwan da zaki nema sune:. 


1.Kanumfari, 

2.Totuwar Rage, 

3.Garin Miski, 

4.Gabaruwa. 


YADDA ZA KI HADA TURAREN 

Dafarko zaki nemi bushashiyar gabaruwarki mai kyau, saiki samu totuwar Rakenki itama mai kyau kuma bushashiya. 


Saikuma ki kawo kanumfarinki da garin miski dinki. Saiki hadesu gabadaya da wannan bushahshiyar bagaruwar ki da totuwar rakenki bushashiya saiki hadasu baki daya ki dake su sosai. 


Wannan hadin shi zaki dinga diban kadan kina tsoguno dashi yan mintuna kafin mijinki ya sadu dake, insha Allah zaki bada labarin dadin wannan hadin ga kawayenki.


Post a Comment

0 Comments