Hanyoyin Kulada lafiyar Yara a yanayin Hunturu.
Sanin kowane dokan jiki na Yara( Immunity) Bai zama fully developed ba.
Saboda hakan abu 'dan 'karami yakan iya haddasa matsala a jikin su. Yanayin Hunturu Yana zuwa da Sanyi(Da Safe da Kuma dare), da Kuma zafi zafi da Rana, da 'kura da iska sosai. Wannan yanayin Yana farawa ne daga 'karshen watan November har tsakiyar March. Saboda wa'yennan abubuwan Dana lisafa da yake zuwa dasu, yakan illata jikin 'Dan Adam. Yana illata Mashaqar iska ta mutum ya saka mura, tari, zubowar majina, zazzabi, numfashi da 'kyar, Yana Kuma illata idanu su rin'ka 'kaikayi, ruwa da ja. Yakankuma saka ha'bo, fitar jini a hanci, la'b'ba su bushe su tsage, qafa ta tsage kirci ya fito, fata ta tsage mutum ya rin'ka hasarar ruwan jiki da sauran illolin da yake iyawa jiki.
Hanyar Kulada Yara ta ha'da da:
1. Tabbatar da anyi cikakken rigakafin da yadace ace an musu.
2. A daina fita dasu, a rufe tagogi da 'kofofi, a wanke curtains, zannan gado, a shafe fanka, teburra, kujeru domin gudun 'kura. Fita da Yara a wannan yanayin yazama kawai idan lalura ta Kama ne.
3. A musu wanka da ruwa masu 'dumi. Idan aka fito wankan a shafa masu Mai, Kuma duk sanda aka chanza pampers a shafa Mai. Kada ashafa musu lip balms na manya domin shanyewa sukaye, suna da irin nasu. Kuma Ana iya shafa Zuma Mai kyau ko sunyi licking Bata masu illa.
4. A saka masu tufafi masu kauri, da safa, da hula domin kariya ga Sanyi.
5. A rin'ka Basu ruwa sosai idan sunfi wata shida, akuma rin'ka Basu kayan itace irinsu kankana da sauransu.
6. Idan mura ta kamasu, ayi anfani da tissue a cire majinar ayi discarding inda wani bazai samu access da ita ba. Idan ko 'kura ta fada a ido, kada a saka 'kyalle ayi anfani da ruwa masu kyau a wanke idanun.Idan muran yayi tsanani, ko zazzabi ko tari yayi tsanani Tau a bi'di gaban Likita.
7. A Hana Yara Wasa da ruwa. Yaro Mai asthma, agayawa Malamai Kuma ya Rika Inhaler inshi.
8. Masu sickler sai akula sosai dasu awannan lokacin sanyin.
0 Comments