Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ILLOLIN YIN BLEACHING GA MATA DA MAZA DA CUTUTTUKAN DASUKE SAKAWA


 **ILLAR YIN BLEACHING GA MATA DA MAZA**


Bleaching shine yin anfani da wani sinadari na cream,lotion,sabulu ko shower gel domin haskaka fatar jiki.wasu lokutan har allura da kuma tablets ana amfani dasu wajen bleaching.


**YADDA SINADARIN BLEACHING YAKE AIKI A JIKIN FATA**


#Sinadarin bleaching baya iya aiki a jikin fatar dan Adam har seya kashe wasu sojoji na musamman da suke a jikin fata.su wadannan sojoji suna bada ingantacciyar kariya ga fatar dan Adam ta yadda kwayoyin cuta basa iya shiga kai tsaye.amma sinadarin bleaching yana kashesu sannan yayi aiki wajen canza launin fata.


Abin takaicin shine wadannan sojoji basa ta6a dawowa idan suka mutu kuma daga sannan babu wata kariya a tare da fatarka.


**ILLOLIN DA BLEACHING YAKE JAWOWA**


#skin cancer (ru6ewa/zagwanyewar fata.


#Makanta.


#Tsananin duhun fata bayan lokaci me tsayi ana bleaching.


#Warin jiki.


#Rashin Nutsuwa.da sauransu.


**6OYAYYAN SINADARIN BLEACHING**


#6oyayyan sinadarin da yake cikin man bleaching wanda ba kowane yasan dashi ba shine;Male sperm(Maniyyin Maza)Wanda ya kasance tacacce kuma ingattaccen sinadarin da yake gyara Jikin dan Adam.


**MENENE MATSAYIN WANDA MANIYYI YAKE JIKINSA/TUFAFINSA?**


#A bayyane yake bashi da tsarki kuma ya zama Najasa abin qyama a gurin Mahaliccinsa(Allah).


#Ba'a kar6ar ibadar mara tsarki komin kyawunta domin tsarki shine cikar ibada.


#Haramunne ya ta6a alqur'ani domin shidin litrafine me tsarki kuma daga waje me tsarki zuwa ga masu tsarki kadai.


#To ina mata da maza masu bleaching?Kuna zuwa masallaci kuyi sallah,kuje islamiyya Ku karanta qur'ani.shin kunsan hukuncinku?Allah kadai yasan azabar daya tanada akanku.


**JAN HANKALU**


#ki/kayi haquri da yadda Allah ya halicceka domin shine yaga dacewar hakan da halittarka kuma yafimu sanin Dede.




Post a Comment

0 Comments