MAGANIN TARI DA MURA NA YARA DA MANYA
A lokacin sanyi ko lokacin sauyin yanayi kamar yanzu, yara/manya suna yawan fama da yawan tari ko mura to Insha Allah ga hanyar magancewa cikin sauki amma a tabbatar tarin na mura ne bana cuta ba.
*BANGAREN YARA:-*
*JARIRI DAN WATA 1 ZUWA 6:-*
Idan jariri ne bai wuce wata daya zuwa shida ba za a samu man tafarnuwa a rika shafa masa a hancinsa da kirjin sa kullum safe da yamma, a kiyaye yi masa wanka da safe ko barin sa iska tana samun sa.
*YARO DAN WATA BAKWAI ZUWA shekara DAYA:-*
A samu man shanu a hada da man zaitun a rika shafe masa hancin sa da kirji sau 2 a rana, sannan a rika diga masa man tafarnuwa wanda aka hada da man hulba,kamar digo 5.
*YARO DAN SHEKARA 1 ZUWA SHEKARA BIYU:-*
Ana samun zuma kamar chokali 5 lemon tsani karami a Raba 4 a matsa rabi akan zumar a rika bashi rabin karamin chokali 1 da safe da yamma..
*YARO DAN SHEKARA BIYU DA RABI ZUWA SHIDA:-*
A samu kajiji, tafarnuwa sassaken marke dai-dai gwargwado, a tafasa a sauke a saka zuma asha sau uku a rana da dumi kamar shayi.
*BANGAREN MANYA SHEKARA 7 ZUWA SAMA:-*
- Na farko a samu kajiji, tafarnuwa sassaken marke dai-dai gwargwado, a tafasa a sauke a saka zuma da lemon tsami rabi asha sau uku a rana da dumi kamar shayi.
- Na biyu ana narka manja original asa suga kadan da lemon tsami rabi asha sau uku a rana.
- Na uku masu fama da tari da mura ko dattin kirji sakamakon taba ko kura sai a samo:-
1. Ciyawar buruku.
2. Citta.
3. Kanumfari.
4. Lemon tsami.
6. Zuma.
A hade number 1 to 3 kowanne garin sa cikin karamin cokali da ruwa karamin kofi 3 a tafasa a sauke a matse lemon tsami mai ruwa babba daya (banda me ulcer) zuma rabin karamin kofi a zuba a flacks ana sha kamar shayi kullum a shanye wannan hadin daga safe zuwa dare har a warke InshaAllah.
0 Comments