Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

MUHIMMANCI DA TASIRI DA SIRRIKAN SAKA JIGIDA A KUGUN MATA DAKUMA ALFANUN SAKAWAN



 MUHIMMANCI  DA TASIRI DA KUMA ALFANUN JIGIDA A KUGUN MATA


Babban alfanun da jigida yake yiwa mata kamar yadda bincike

ya tabbatar a wannan lokacin shine, yana karawa mace fadin

kugunta ga irin matan nan da suke da karancisa.

Maza da dama da aka zanta dasu sun nuna sha’awarsu na

ganin matansu na aure suna saka jigida domin yana karamusu

kyau musamman idan mace tana sanye da kayan da zasu

bayyanasu.

Har ilayau cikin alfanun da jigida ke dashi shine yakan motsa

sha’awan maza a yayin da suka ji sautinsa ko suka hango

shatinsa.


Kara ko sautin dake fitowa daga jigida a lokacin wasannin

motsa sha’awa da kuma lokacin gudanar da jima’i abune dake

himmanta maza yake kuma kara musu kuzari da azama.

Sai dai duk da wadannan tasiri, mahimanci da alfanun da jigida

ke dasu ba duka mata bane suke sanyawa ba, haka ma maza

da dama basu son ganin mace da jigida. Wasu mutane sun

riga sun kudura cewa duk mace ko budurwar da aka ga tana

sa jigida ko akaji sautinsa a tare da ita suna daukanta mutuniyar banza, wanda yin hakan babban kuskure ne.

Shi dai shan koko daukan rai ne. Abincin wani, gubar wani.







Post a Comment

0 Comments