Shin yan uwa Kunsan illar raba daKi da miji?
Toh Ku saurara Kuji:-
1- yana rage Kusanci Ko shaKuwa a tsaKanin ma'aurata.
2- yana sa ma aurata su rika jin wani iri wajen neman juna don kauda sha'awarsu ko raya sunnah mace zata ki zuwa wajen mijinta tace ai idan yana da bukatarta ya nemeta, shi Kuma miji ya hakince a dakinsa yaki zuwa wajen matarsa yana jira sai ta biyoshi, karshe sai dai su rungumi Pillow su kwana suna jin haushin juna.
3- yana sa fada yayi tsawo a tsakanin maaurata idan sun samu sabani, sai a dauki kwana ki basu shiryaba.
4- yana sa miji ya samu daman yi wa matarsa iyaka da wasu abubuwanshi ababen cikin dakinsa
5- yana sa mace ta rika jin dar-dar duk lokacin da ta shiga dakin mai gida da niyyar kwalema ko neman wani abu, musamman idan ya shigo ya tarada ita a ciki dakinsa tana dube-dube Ko neme-nemen wani abu
*_HIKIMAR KWANA DAKI DAYA DA MIJI:-_*
1- yana sa shakuwa da karin sabo
2- yana sa tausayi da sanin halin da Partner ke ciki a cikin awoyin bacci.(incase daya daga cikinsu zai samu nyt fever, bad dream ko Wani attacK cikin
HATTARA DAI MA'AURATA
HIRAR DARE
mu Lura da wannan 'yar'uwa Mata, hirar dare nasa maigida ya daina fita yawo da daddare, Saboda baya samun hirar dare daga Gare ki, Kuma Galibi idan suka fita, sai sun raba dare Ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke Kuma sannan Kinyi barci.
Kinga irin wannan Ina amfaninsa.
Kin dinga jawo hankalin maigidanki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar Banza kamar zina, debo cuta, shan giya da sauransu.
A Kullum Bayan sallah Isha, idan aka ci abinci, sai a dasa hira, Har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to Yau da Kullum idan ya ga ki Na yawan damunsa da hirar.
To Zaki ga ya dawo yana so, muddin kika saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba, Amma idan kika yi saka ci ya saba da fita, to duk Randa kika so ya Bari, ba zai Bari ba.
SANA'A GA MATA
kiyi kokarin yin Sana'a koda kuwa ba ki da jari Mai karfi, to ki yi da Dan Abinda kike da shi, Saboda zama haka ba shida dadi, gara a Dan dinga Neman abin dogara da Kai kuma idan kina nema ki dinga taimakon maigida koda ba shine, idan ya samu ya biya zai dinga jin dadi Kuma zai kara sonki, Saboda tallafa masa da kike yi.
Dan Maggi, da sauran bukata.
Mu dage mu nemi Sana'a yar'uwa zama haka ba Bamu bane, tunda wani namiji Ko yana da shi, ba zai dinga Baki Kullum ba, kin ga Ko idan kina Sana'a Zaki tallafa ma kanki da 'ya'yan ki,Kuma Zaki rage samun matsaloli tsakanin ki da maigida.
SHAWARA
yan'uwa Mata ga shawara garemu Baki daya, idan muna Sana'a, tofa gaskiya mu Lura mu rage yawon zuwa kasuwanni Ko Kuma mu fita zuwa kasashen ketare sarin Kaya ! Gaskiya ire-ire wadannan basu dace damu ba, Saboda Ko muna yi tsakanin da Allah, to a duniya ba kowane zai yarda da hakan ba.
Wasu ma sai Kaga mace ita kadai Ce a wurin mijinta daga ita sai 'ya'yanta, Amma ta Kasa zama ta Lura dasu da tarbiyyansu, to ire-ire wadannan duk hanyoyi ne Na nemo matsala tsakaninki da maigida Don kuwa muddin Sha'awa ta dame shi.
To watakila yaje ya nemo a waje, ke Kuma ki Na can kina yawon Sana'a Ko Kuma ya kara aure, Kinga kenan an sha dake, to gara mu rage, Saboda Ko kin bar mai ,Mai aiki , ba zata kula dasu kamar ke ba.
KI ZAMA MAI BOYE SIRRIN KI
kiboye sirrinki ga iyayenki, iyayen mijinki, yarki, "Yan'uwanki, da sauransu, karki zama komai aka yi a gidanki, idan wani naki yazo, sai kin Fada masa, Ko Kuma ke ki zari gyale da takalmi kije ki Fada.
Wannan ba Abu ne Mai kyau ba, muguwar dabi'a Ce,Kuma kina rage ma kanki mutunci da daraja da soyayya a idon mijinki da idon jama'a Baki daya.
Kuma idan mutane suka ganeki, zasu dinga zundenki, suna miki tsegumi, Don haka ki soyayya a idon mijinki da idon jama'a Baki daya.
Kuma idan mutane suka ganeki, zasu dinga zundenki, suna miki tsegumi, Don haka ki zama Mai sirrin, musamman ma ga iyayenki, sai zaman lafiya, ya wadace Ku da mijinki da kishiyarki radam! Amma iyayenki basu manta ba, Saboda an Ce tsakanin miji da Mata sai Allah.
Komai yana bukata sirrin, Kuma maigida zai dinga gaya miki magana, ba tare da yana shakka ba, Saboda ba Zaki Fada ma wani ba.
0 Comments