ADO DA KWALLIYA GA MATA DA YADDA ZAKIYI ADO DA KWALLIYAR
Assalamu Alaikum yar uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin zauren namu na Duniyar Fasaha insha Allahu yau zanyi bayanine akan sirrin kwalliya da kowace ya mace ya kamata ta sani a rayuwarta, yin kwalliya tare da sanin fai’dodinsa da kuma sirrinsa yana da matukar amfani, Mata da dama na son sanin sirrin da ke sanya kowacce kyau. A gaskiya zamani ya kaimu lokacin da babu mace mummuna sai dai in ta ga damar zama mummuna. Akwai sirrin kwalliya da dama, ta yadda duk munin mace idan har tana kulawa da su, zai yi wuya a ga muninta. Shi ya sa wasu mazan ke bai wa junansu shawarar gane kyakyawar mace, domin kada a zo a yi zaben tumun dare. Idan mace ta zama mummuna ita ta so. Akwai ababe da dama da ake gyarawa daga yanayin shafa hoda da jan-baki da ja-gira da sauransu.
Sirri na farko shi ne; mace tasan irin girar da ya kamata ta ja a fuskart a. Misali, idan ke mai fadin fuska ce ja-girarki bai kamata ta yi kama da na mai doguwar fuska ba. Ja-girar mai doguwar fuska ba ta da fadi. Amma na mai fadin fuska za a samu da fadi.
Kwalliyar mace mai fadin baki kuma daban take da mace mai tsukakken baki. Mai tsukakken baki ko me ta shafa ana ganin kyawun shi, ba kamar mai fadin bakin ba. Yana da kyau idan ke mai fadin baki ce ki samu gazal din baki, ki ja layi a bakin kafin ki shafa walau jan baki ko man baki. Yin hakan na rage fadin bakin.
Mace mai manyan idanu da wadda ke da kananan idanu tabbas kwalliyarsu za ta zama daban. Mai manya idanu ko ba ta shafa komai ba za ta ganu, kuma tayi kyau. Amma mai kananan idanu sai ta shafa hodar kan ido (eye shadow) domin fito mata da hasken idanunta.
Kyawun mace mai hanci daban take da mai gajeren hanci. Albishirinku mata! Yanzu akwai hodar da ake shafawa domin mikar da hanci, musamman ma masu gajerun hanci, amma da dan tsada. Kuma za a iya samun irin wannan hodar a manyan kantunan da ake sayar da kayan kwalliya.
Mace mai kumatu daban take da wadda ba ta da shi; mara kumatu za ta iya shafa hodar ‘blush’ domin inganta kumatunta da kuma kara mata kyau. Mai kumatunma za ta iya shafa wannan hodar, amma sai ta ga dama domin in ta bari a hakan ma kyau za ta yi.
0 Comments