gyaran fuskar mutum kamar haka:
1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin.
2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska Danyen ƙwai.
3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje.
4- Danyen kwai na kara ma fuska haske.
5- Ruwan kai na rage kumburin idanu Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.
Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.
Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.
0 Comments