♜ *GYARAN JIKI* ♜
( fatan ta yi laushi da sheki)
■ man zaitun
■ lalle
■ kur-kur
■ madara peak.
Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki.
♜ *GYARA JIKI 2* ♜
Wannan hadin shi akecewa kafi TURGEWA.
➽ kur-kur
➽ dulka
➽ zuma
➽ kwai
➽ lemun tsami.
Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki.
Idan kuma har dajiki kikeso, sai ki shafa harda jiki Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge.
♜ *GYARA JIKI 3* ♜
( fata ta yi laushi da sheki)
✥ lalle
✥ kwaiduwar kwai guda 3
✥ manja cokali 3 kur-kur.
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka.
♜ *KYAN FUSKA* ♜
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi.
⇎ dettol
⇎ sabulun Ghana
⇎ garin zogale
⇎ farar albasa.
♜ *GYARA FUSKA* ♜
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takun Kore kurajen fuska bawon kankana
A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul.
*GYARA FATA*
□ Lemun tsami
bawon kwai
kur-kur.
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske.
*GYARA FATA*
● ganye magarya
● sabulun salo.
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki.
*GYARA FATA*
• ganyan magarya
• man zaitun
• man habbatussauda.
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran.
*GYARA FATA*
◈ lalle
◈ garin ridi.
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka.
★★ *MAGANIN TABO A JIKI*☆☆
Ki samu khai babban cokali daya sai ki hada da ruwa Kofi biyu ki tafasa bayan ya huce sai a rinka shafawa a jiki da fuskar.
■─ *AMFANIN* *KUR-KUR*─■
➧ yana da amfani sosai awajan gyara fata ko jiki
hakan nema ya saka muka gane muku wannan
hadin na gyara jiki.
➮ kurkun
➮ dakakkiyar alkama
➮ man zaitun
➧ Ki samu kurkun sai ki daka, daga nan sai ki hada
da dakakkiyar alkamanki, sannan ki hada da man
zautun daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a
jikinki bayan awa biyu ko uku sai ki wanke
fuskarki ko jikinki da ruwan dumi..
☆ *MAGANIN NANKARWA* ★
( strech mark)
Nankarwa shine irin wannan zanen da yake fitowa a cikin mace da zaran ta fara haihuwa ko kuma in tayi kiba A ciki mace ya kan fitowa ya sanya fatar cikin duk ta yamuste ana amfani da man dodon kodi a shafa a ciki,yana gyara fatar ciki ta koma kamar ba ta haihu ba.
2
● man kadanya
● man zaitun
● Lemun tsami.
Ki hada man kadanya da man zaitun guri daya, ki matsa lemun tsami a kai, amma ba da yawa ba,ki matsa sosai sannan sai ki dinga sharewa ki yawaita yi.
Ana shafa zuma farar saka da daddare, idan zaki kwanta barci da safe sai ki samu ruwan dimi ki wanke.
0 Comments