YADDA ZA'A MAGANCE WARIN BAKI DA SAMUN HASKEN HAKORA
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
dan kina goge haqorinki sau biyu a rana zai yi haske kamar haka A wannan makon na kawo miki bayanin yadda za ki lura da hakorinki, wato- cire dattin hakori da kuma kara wa hakorinki fari da kuma lafiya.
Ana so ki rika wanke bakinki da man goge baki ko aswaki akalla sau biyu duk rana, hakan zai sanya hakorinki ya yi haske.
Idan kina da dattin hakori sai ki nemi man goge baki kamar daya daga cikin wadannan: Colgate da Rembrandt da 3D Crest da Listerine da Akuafresh da sauransu, sannan kina goge hakorinki da shi.
Za ki iya amfani da bakar soda (Baking Soda) wajen goge hakorinki sau biyu a mako. Kadan ake so ki rika diba idan za ki yi amfani da sodar.
Sannan bayan haka ana bukatar ki kuskure bakinki sosai bayan kin kammala amfani da sodar. Kada don kina amfani da wadannan sinadaran sai kuma ki daina goge bakinki kamar yadda ya kamata.
Ki rika amfani da kororon da ake shan jus ko lemon kwalba wajen shan jus ko lemon kwalba, hakan zai kara wa hakorinki fari da haske. Ya kamata ki rage yawan shan kofi da kuma shayin da ba a hada da madara da sauran kayan hadi ba, domin rashin yin hakan zai kara wa hakorinki datti. Ki guji shan abu mai tsananin sanyi ko zafi, hakan zai taimaka miki wajen kara hasken hakorinki. Ki guji yawaita shan abu mai siga domin kauce wa rubewar hakori.
Ki rika amfani da tsinken sakace hakori bayan kin ci abinci, musamman idan kin ci nama ko kifi da dai sauransu. Rashin yin hakan zai sanya sauran abinci ya taru a matse-matsin hakorinki, wanda kuma zai iya janyo wa hakorinki rubewa ko kuma ya yi duhu, ko ya haifar miki da warin baki.
0 Comments