Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAMANTAKEWAR AURE YA KAMATA TA KASANCE GA MA'AURATA CIKIN KAUNAR JUNA DA SOYAYYA


YADDA ZAMANTAKEWAR AURE YA KAMATA TA KASANCE GA MA'AURATA:

1.  Abu na farko da ya kamata ki sa ni kuma ki kiyaye Shi ne Darajar  mijinki da kuma ganin Girmansa da kimarsa, Anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar Auratayya,Domin Daga lokacin da Aka Daura Miki Aure da Shi To Ya Zama Tamkar Mahaifinki da Mahaifarki, kar wai Dan kina ganin ya zama kamar Abokinki ki rainashi, a'a Anfi so Mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban a Cikin zuciyarta da kuma fili.


2.  Na biyu kuma Shi ne ki Girmama Iyayensa da 'Yan Uwansa tamkar Yanda za ki Girmama naki iyayen da 'Yan uwan kar ki kuskura kiyi aiki da Wannan karin maganar Wacce Hausawa ke Cewa "'ba a iya Musu 'Yan dangin miji"', Duk namiji Yana san a Girmama Iyayensa da 'Yan uwansa.


3.  Abu na Uku Shi ne ki zama mai Mutuqar hakuri da juriya a Gidan aurenki, Domin zaman aure zama ne na hakuri da Kuma kawaici, ki k'i ji ki k'i gani sai ki zauna lafiya da mijinki.


4.   Abu na Hudu kuma Shi ne kar ki zama Daya Daga Cikin matan nan masu bayyanar da Sirrin mazajensu da Sirrin Gidan aurensu ga kawaye ko kuma Abokan Gaisawa hakan Haramun ne.


5.  Sai Abu na Biyar Shi ne ki kasance mai tattalin Dukiyar Mijinki, Ma'ana Banda Almabazarancin da kayan miji, ki kasance Mai tattalin Dukiyarsa da Kayansa Domin Kowanne Namiji Yana kin jinin Yaga Yasha Wahala Ya Nemo Abu Sannan An  Wulakanta.


6.  Abu na Shida Shi ne kar ki zama mai Yawan bin Kwakwkwafin Mijinki, Komai Yake Yi Idonki da Kunnenki Akai, kar ki zama haka Domin Maza Basu kaunar Mace Mai Bin Diddigen Abubuwan Da Suke Yi.


Karin-Bayani:.  Wadannan Abubuwan Guda (6) Da na lissafo da ma Wadanda lokaci Bai bani Damar fada ba Yana da kyau Ga Matar-Aure Mai Hankali, da Wayo da Dabara da Kuma Ilimin Zamantakewar-Aure Ta Rikesu Kam Kada Tai Sakaci da Su, Domin Gaba Daya Rayuwar Aure a Cikin Su Ta ke,Kuma Duk Wacce Tai Riqo da Su Kuma Ta Aiki Dasu Insha Allahu Babu Ita Babu Shiga Matsalolin Da Mata ke Fuskanta a Gidan Mazajen Su,Kuma Koda Allah Ya Jarabceta da Azzalumin Miji Insha Allahu Allah Zai Tseratar da Ita Daga Dukkanin Sharrinsa.Daga Karshe Kada ku manta Da Cewa Haquri da Juriya Shi ne Kan Gaba Domin Shi ne Tsanin Da Za ki bi har ki Kai ga Cin Nasarori a Rayuwarki.






Post a Comment

0 Comments