Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ABUBUWAN DA YAKAMATA KINAYI TARE DA MIJINKI KUMA KUKASANCE DA KAUNAR JUNANKU AKODA YAUSHE


 YADDA SOYAYYAR MIJI DA MATA YAKAMATA YAKASANCE ACIKIN GIDAN AURE CIKIN NISHADI DA KAUNAR JUNA



 •  Mace da mijinta su rinƙa cin abinci tare, kuma shi ya rinƙa bata da hannunsa, itama ta rinƙa bashi da hannunta.


      wannan yana sawa namiji bazai rinƙa jin daɗin cin abinci a wajeba, haka itama bazata cin abinci ita kaɗai ba saita jirashi yadawo.


•  Idan zaisha ruwa kada kibarshi yasha da kansa, kaima ka rinƙa bata ruwa da hannanka tanasha kuma a hankali kana rarrashinta,


      Hakan zaisa duk lokacin da zaisha ruwa a waje ko idan zatasha ruwa  zaku rinƙa tunawa da juna.


•  A wasu lokutan idan kabata ruwan kace kada ta shanye kanaso kasha ruwan dake cikin bakinta, kuma ka haɗa bakinka da nata kasha ruwan daga bakinta, kema ki rinƙa yi masa haka, wannan yaka ƙarfafa ƙauna.


•  Miji ya rinƙa sakawa matarsa kaya, haka kema ki rinƙa sakawa mijinki kaya idan kunyi wanka, kuma idan za'a cire kaya ka rinƙa cire mata, kema ki rinƙa cire masa kaya.


      Wannan yana sawa ana kasa mantawa da juna duk lokacin da ɗayanku zai cire kayansa idan baya tare da abokin rayuwarsa zaiji babu daɗi, saboda zaita kowa zaita zumuɗin ɗan uwansa.


•  Ku rinƙa zama ajikin juna idan kuna zaune, ko kuna kallo ko hira, kuma ka rungume matarka koda yaushe idan zakayi magana da ita, koda kuwa tana cikin halin haila ne, 


    Haka kema ki rinƙa rungume mijinki a koda yaushe kidaina nisa dashi.


     Wannan yana sawa koda ɗayanku yayi tafiya ya kasa samun nutsuwa har sai ya dawo gurin abokin rayuwasa.


•  Ku rinƙa wanka a tare, kana wanke mata jikinta, itama tana wanke maka jikinka, hakan zaisa bazaku rinƙa ganin laifin junaba.


•  Ka rinƙa goya matarka lokaci-lokaci idan batai maka nauyiba, kema ki rinka goya mijinki lokaci-lokaci idan har baiyi miki nauyi ba.


      Wannan yana taimakawa wajen kawo zaman lafiya da tausayawa juna.


•  Ka rinƙa bacci a rungume da matarka, kema ki rinƙa rungume mijinki a yayin baccinku, 

 

     Wanna yana sawa miji da mata basa iya fushi da juna, ko anyi fushi, idan lokacin bacci yayi sai an shirya.


•  Idan zakuyi kwanciyar aure, ku rinƙa farawa da wasanni a ƙalla kamar awa ɗaya hour ko sama da haka ana wasa da jikin juna, 


      Domin wasanni suna taimakawa na miji da mace, su ƙara son juna da ƙaunar juna, kuma yana sawa su gamsar da juna sosai.


•  Bayan angam kwanciyar aure kuma a nunawa juna anji daɗin juna tare da nuna farin ciki wa juna da kuma godewa juna, da zuga juna saboda yadda kowa ya gamsar da abokin rayuwasa.


•  Idan mijinki zai fita aiki ko kasuwa ki rinƙa rakashi har bakin ƙofar gida kuma ki tsaya kiyita kallonsa kina masa murmushi harsai kindaina hangshi, haka kaima ka rinƙa juyowa kana yi mata kiss akan iska harsai ka daina hangota.


•  Idan kaje gurin aiki ko kasuwa ka rinƙa turo mata da saƙon soyayya ta waya, ko kuma ka rinƙa kiranta kanajin halin datake ciki, haka kema ki rinƙa kiransa kina yi masa addu'a.


ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.


Dan ALLAH masu aure daga cikinmu ku rinƙa aiki da shawarwari da ake baku.


Mun lura cewa maza anfi samun ƙauyenci daga gareku wajen sakin jiki kuyi rayuwa cikin nisahaɗi da matanku, wannan kuskurene.



Post a Comment

0 Comments