ABUBUWAN DA YAKE HAIFAR DA MATSALA TA KARANCIN RUWAN NAKUDA GA MATA MASU CIKI A LOKACIN HAIHUWA
Kamar yanda mukai bayani a jiya wasu dalilai na haifar da wannan yanayin na KARANCIN Ameniotic Fluids lokacin da Jinjiri ke girma ko lokacin haihuwa Wanda wannan yake haifar da wasu matsaloli ga Mata daga ciki akwai kasa haihuwa dakai, Yazama mace dole sai an Mata aiki ancire Dan.
MANYAN ABABEN DAKE HAIFAR DA WANNAN nada yawa ga kadan daga ciki.
1- Hawan jini, idan Mai ciki ta hadu da hawan jini yana iya haifar Mata da wannan matsalar.
2- Rashin Isashshen Ruwa a jiki, ko Kuma zubar ruwa Mai yawa kafin haihuwa, akwai matan da suke ganin ruwa akalla kwanaki 7 kafin haihuwa wannan matsalar Yana karar da Ruwan NAKUDA kafin haihuwa ta bijiro ya zama mace ta kasa haihuwa da kanta.
3- Rabewar Uwa da Mahaifa,
4- Kafin Haihuwa a samu matsala ta Placenta Abruption.
5- Da sauran cutuka da mafi yawan Mata masu ciki Kan hadu dasu lokacin ciki Allah ya Kyauta.
MATAN DA AKA TABBATAR KO SUKA FAHIMCI SUNA DA KARANCI RUWAN NAKUDA KO AMENIOTIC FLUID MEYA DACE SUYI A GIDA KAFIN HAIHUWA ??
Kamar yanda nai Baku bayani a baya, duk da Naga wasu sunyi Anfani da Rubutun sun canja Masa kama daga karshe sun tabbatar wa duniya su sukai Rubutun oh ni Kabir Danwuri.
Ga kadan daga cikin hanyoyin da ake Anfani dasu Dan Samar da ruwan NAKUDA yanda da zai fito cikin sauki.
1- Yawan Shan Ruwa, Rashin Shan Ruwa ko zama da kishi Yana saurin haifar da wannan yanayin ga Mata masu ciki.
2- Anfani da ainahin kalar Ruwa da ake sawa masu wannan matsalar kadai wato Ivf Amnioinfusion, da zaran an fahimci wannan matsalar Yana da kyau a dora mace akan wadannan Ruwan da dawo da martabar ta da abunda take dauke dashi kafin haihuwa.
3- Mayar da Ruwan jiki Bayan la'akari da Wanda jiki ke bukata Bayan wasu Aune Aune da matsalolin da aka tabbatar idan akwai su.
4- Magance Matsala wacce aka tabbatar da akwai Kama daga Zazzabin Cizon Sauro ga Mata masu juna biyu, Ulcers, Hypertension da sauran su.
5- Samun isashshen Hutu, Dan Allah Mata ku hakura mu kara Aure dan ku samu hutun da ake bukata 🤭🤭🤭😀😀, Yaushe Mace na fama da ciki dake dake Kuma ga aikin Gida.
6- Kula da Kuma Sa Ido daga mu magidanta da Kuma likitocinmu, Akwai bukatan likitoci su rika kula da clients dinsu wato masu ciki.
7- Akwai Kuma bangaren abinci, Yana da kyau Mu magidanta Musa Ido, Mu bude bakin aljihu, Kayan Marmari, kwalama, da Dan abun Dadi duk suna bukata da Allah.
Vegetables kamar cucumber, lettuce, spinach, radish, broccoli da cauliflower suna taimakawa,
Fruits Kuma kamar strawberries, watermelon, tomatoes, cantaloupe/muskmelon da grapefruit.
0 Comments