Turaren wuta na Dambu mai (coconut) Mai kamshi ga kama daki
Iccen dambu 1kg
Garin misik 1tbl spoon
Madaran turaruka
Sugar gwagwani 1 da rabi
Ruwa quarter cup
Sandal powder 4tbl spoon
Ruwan turaren bakhur gora qarami daya
Dafarko kijuye iccen dambu ki tray,saiki tsince datti ki dauko roba ko Kwanu ki jika shi da ruwan turaren bakhur ko amaria,ki rufe ya kwana,Saiki dauko sugar kisa a tukunya yayi brown sai ki Zuba ruwa
Ya kara hade jikinshi,sai ki dauko iccen dambu ki da kika jika ki juye kiyita soya wa har ya soyu ki sauke
Sai ki juye me maiko ki da garin sandal ki juya
Sai ki dauko madaran turare ki Zuba ki kawo misik dinki ki Zuba shikenan kin gama.
Karki cika sugar Dan in kin cika baze yi kaman dambu ba
Sannan Kuma karki cika ruwan a sugar
Kuma kisa madaran turare isasshe.
0 Comments