Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KA'IDOJI DA LADUBBAN TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI


 LADUBBA DA QA'IDAR TARBIYYAR YA'YA A MUSULUNCI.

_______________________________


قاعدة تربوية مهمة في التعامل مع الأبناء، وهي قاعدة: [ لاعبه سبعاً ثم أدبه سبعاً ثم صاحبه سبعاً ] .


Qa'idar Tarbiyyar 'Ya'ya

1. Kayi wasa da su shekara 7.

2. Ka Ladabtar da su shekara 7.

3. Ka Abokance su shekara 7.


1. Wasa Shekara 7; a nan Malaman tarbiyyar musulunci suna cewa za'a mu'amalanci 'ya'ya, mu'amala ta wasa da su, tun daga haihuwar su har sai sun kai shekaru 7.


2. Ladabtarwa Shekara 7; Malaman tarbiyyar musulunci suna cewa daga yara sun kai shekara bakwai (7), za'a fara basu ladabi: ta hanyar nuna musu kaza dai dai ne, kaza ba dai dai ba ne, ta hanyar tsawatar musu, ta fuskan bugu mai sassauci, ta hanyar koyar da su addinin su, koyar da su azkar, Sallah, da sauran su, za'a yita yin hakan har sai sun kai shakara 14.


3. Abokanta shekara 7; daga lokacin da suka kai shekara 14, to a nan fa girma ya fara zuwa, anan ne kuma abokai suke fizgan yara daga tafarki na gari, daga nan ne yaro zai fara jin cewa yafi qarfin kowa, to ana so a lokacin mahaifi sai ya mayar da yaron ya zamo abokin shi, in zaije gaisuwar rasuwa ya tafi da shi, in zai je ziyara ya tafi da shi, in zaije wajen karatu ya tafi da shi da sauran ayyukan alkairai. Har sai ya kai shakara 21. 


Daga nan kuma In sha Allah yaro zai kasance a tafarki na gari, sai dai kuma yadda malamai sukayi da shi, ko ya shiga hanun na gari kokuma hanun 'yan hayaniya. 


Allah yasa mu dace, Allah ya bamu yara na gari, ya shiryar da mu, ya kare mana al-umma.



Post a Comment

0 Comments