ME MIJINKI YAFI SO A GURINKI.
"Mata da yawa ba sa fahimtar menene abin da mazajen su suke so a tattare dasu har sai sanda mazajen suka buɗi baki suka furta musu, kai da yawansu ma ko mijin ya furta musu irin ababen da yake son matarsa ta lazimci yi masa su, matan ba kowace ce take iya jurewa ba"
-
"Haƙiƙa kuwa rashin fahimtar irin abinda mijinki yafi ƙauna daga gareki zai rage muku jin daɗin rayuwar auren daga ke har shi ɗin, kuma da yawan maza rashin samun cikakkiyar kulawa daga matayen su na gida ne ke sawa su koma bin matan banza a waje"
-
"A matsayin ki na matar aure, idan kina tare da mai gidanki, to ki tsaya ki natsu ki fahimci abin da mijinki yafi ƙauna daga gareki, sannan sai ki lazimci yi masa shi. ki tsaya ki fahimci irin kalaman da yafi so ki dinga furta masa, sai ki dinga faɗa masa su, ki fahimci abinda yafi jin daɗin taɓawa a jikinki, sai ki dinga bijirar masa dashi, ki fahimci abin da yafi ƙaunar gani a jikinki, sai ki lazimci bayyanar masa dashi, ki fahimci irin hirar da yafi ƙauna ku dinga yi idan kuna tare, sai ki fara yi masa, muddin kika lazimci yin hakan, to in sha Allahu za ki zauna ƙalau da mijinki"
0 Comments