Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA MATA ZASU GYARA BREAST DINSU DA KUMA JIKINSU BAKIDAYA HADI MAIKYAN GASKE


 *HADIN GYARAN NONO DA JIKI BAKI DAYA SATI BIYU KAFIN YAYE*


Dole ne duk inda mace take to ta matso kusa ta jarraba wannan hadin InshaAllah za tayi mamakin yadda jiki zai gyara musamman nono da aka shayar da yaro. 



*GARGADI*

*Magungunan bature ko supplements masu saka kiba, nono, hips, matsi, sha'awa, ni'ima uwa uba fari nada illa matuka a lafiyar ku dan haka idan kunne ya ji jiki ya tsira. 

Wannan hadin da za mu bada yana da matukar amfani ga jikin mace, amma sai masu hakuri da bin ka'idar sha ne kadai za su rabauta. 



*Abubuwan bukata:-*

1. Waken suya gwangwani 4. 

2. Alkama gwangwani 4.

3. Dawa gwangwani 4. 

4. Shinkafar tuwo gwangwani 4. 

5. Ridi gwangwani 4. 

6. Agushi gwangwani 4.

7. Aya gwangwani 4. 

8. Gero gwangwani 4. 

9. Gyada me bargo gwangwani 4. 

10. Hulba gwangwani 2. 



Duk abun dana lissafo kar a tambaye ni a soya dan ban ambaci suya a ciki ba. 



Za a hade kayan dake sama tas bayan an tabbatar da tsaftacewa sai a nika suyi laushi sosai. 



Za a samu ruwa 75cl a dora wuta sai a debi garin da aka nika a dama da ruwa 25cl a zuba a kan ruwan dake wuta bayan ya tafasa, sai a rufe a bashi a kalla minti 10 zuwa 15 a tabbatar ya dahu a sauke a saka madara asha da safe kan aci komai da rana kan aci komai da dare in za a kwanta. Ba a dafa da yawa a ajiye zai tsinke. Idan miji na fama da rama ko rashin ruwan mani yana sha sau daya kullum idan yaro na rama ko za a yaye shi a bashi sau uku kullum idan be karbe shi ba yana saka shi kashi a cire hulba da madara InshaAllah zai dena. 

Mata masu son kiba su sha matan da iya nono suke su ya gyaru su cire number 1 to 5 suyi ragowar.




Post a Comment

0 Comments