Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YANDA AKEYIN GYARAN GASHI DA ALOEVERA GASHINKI YAYI TSAWO KYAU DA SHEKI


 YADDA AKE GYARAN GASHI DA ALOE VERA YAYI KYAU TSAWO DA SHEKI

 

aloe vera na dauke da abunda a turance ake kira da prolytic enzymes su wannan enzymes din suna gyara matattun cells din da ke saman fatar kan mutum ta hayar rage bushewa, yawan kaikayi da kuma yawan man dake taruwa a saman fatar kan mutum. wanda shi wannan man ke haduwa da datti ya chakude ya toshe kafofin gashi tare da hana gashi fitowa.


MAN ALOE VERA

wannan farin ruwan mai kauri da yake cikin aloe vera bashi bane man aloe vera shi wannan sunan sa ALOE VERA GEL sanan akwai wani ruwan dorawa dorawa (yellow) a jikin sa da ake kiran sa da ALOE VERA LATEX wanda shi wannan latex din yana da matuqar daci kuma yana bata ciki sosai.

Aloe vera ba kamar sauran shuka bane ba'a iya fitar da mansa shi kadai dole sai an hada da wani mai kamar zaitun, man kwakwa da sauran su.


YANDA ZA'A HADA MAN ALOE VERA (ALOE VERA OIL):


Abubuwan bukata sune ___


🍀- aloe vera rabin kofi

🍀- man kwakwa ko zaitun rabin kofi

🍀- lavenda, jojoba, jasmine, peppermint ko rose oil digo (drops) biyu ko uku 


1-ki bare aloe vera din sai kisa chokali ki kwashe farin ruwan ciki (aloe vera gel) idan kin Ci karo da wani ruwaruwan dorawa to ki gujesa dan bashi da kyau. ki kwaba shi sosai da man kwakwan. ki jujjuya sannan ki rufe ki barshi na tsawon kwana biyu ( ki ajiye a wuri mai duhu kuma marar zafi sannan kuma ba mai sanyi da yawa ba. )


2-ki juye hadin a cikin tsaftatacciyar tukunya

3-dora tukunyar a wuta na tsawon minti goma kina yi kina juyawa kuma kar ki cika wuta 

4-sauke ki bari yayi sanyi sannan ki diga man lavender ko wanin sa sau biyu tal ko uku (kamshi yake sawa musamman dan aloe vera oil na tausa za'a hada)

wannan hadin ana amfani dashi a ilahirin jiki da kuma gashi sai dai ba zai wuce tsayin sati biyu ba. Sannan kada a ajiye shi a waje mai zafi da yawa.


MAN WANKE GASHI NA ALOE VERA (ALOE VERA SHAMPOO):


Abubuwan bukata sune :


🍀-aloe vera gel rabin kofi

🍀-liquid castile soap (abun hada sabulu na ruwa) kwatan kofi

🍀-man zaitun chokali daya

🍀-man rosemary digo (drops) 10

🍀-man peppermint digo 10

🍀-man bergamont digo 10

🍀-roban shampoo wanda ba komai aciki


YANDA ZA'A HADA

za'a zuba duk wadannan kayan hadin cikin roban shampoo din a rufe da kyau sannan ayi ta jijjiga shi sosai na tsawon lokaci.


ALOE VERA HAIR MASK:


Abubuwan bukata:


🍀-aloe vera gel kofi daya

🍀-man cika-gida (castor oil) chokali 2

🌿-garin hulba chokali 2

1-ki zuba a blender a markada shi sosai 

2-juye a roba a shafa maki shi tamkar relaxer (man famin)

3-ki rufe kan da leda sannan ki daura dan kwali ki kwanta dashi sai da safe ki wanke zai taimaka wurin tsawon gashi insha Allah.


ALOE VERA HAIR MASK (NA MAGANIN KARYEWAN GASHI):

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿


Abubuwan bukata:


🍀-zobo chokali 2

🌿-aloe vera kofi daya

Nikasu wuri daya a shafa a gashi na tsawon awa daya sannan a wanke.


ALOE VERA HAIR MASK ( NA TSAWON GASHI)

Abubuwan bukata

-kwoi guda biyu

-aloe vera gel kwatan kofi

-man kwakwa chokali daya

-man rosemary digo 6

ki zuba su a roba tsaftatacce a sa maburgi mai tsafta ko kuma whisker a burge shi da kyau. 

sannan a shafa daga fatar kai zuwa karshen gashi. 

a nannade gashin da hulan wanka ko leda bayan hakan na tsawon minti 15-30 sannan a wanke.

wannan shine takaitaccen abunda na sani game da aloe vera a gashi.da wannan nake fatan duk mai wata tambaya zai kokarta ya turo tambayar sa kafin wucewar sati biyu.



Post a Comment

0 Comments