Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

DABARUN INGANTA TARBIYYAN YARANMU DA KUMA YADDA ZAMU JASU AJIKI


 DABARUN INGANTA TARBIYYAN YARANMU DA KUMA YADDA ZAMU JASU AJIKI.


A matsayin ki na uwa wani irin rawa kike takawa Dan ganin Tarbiyar yaranki ya tafi successfully ba tare da an samu matsala ba


Domin kulawa da yaro da bashi tarbiyar daya kamata hakuri ya zama dole awajenki


Saboda kina tunanin kin dage kina tarbiya Amma wani nacan waje yana warware miki tufkan da kikeyi.


Ki manta da cewa yaranki basa fita waje kullum suna gida sai makaranta to wlh a makarantar ma zaki samu wanda zai warware miki Tarbiyar da kike ba "ya_yankiKi sani acikin matakan Tarbiyar yaranki babu duka aciki, kuma babu zagi aciki


Abubuwan da ake buqata shine

_Addua 

_tsawatarwa

_Waazi cikin wasa da dariya

_Barazana dss


Dole koda kinama yaranki tarbiya ya zama dole ki hada musu da Addua domin itace gaba akan komaiTsawatarwa Shima yanada muhimmanci sosai Amma ba irin wannan zaki firgita yaro har ya fita hayyacinsa ba


Sannan wa'azi, misali cikin wasa da dariya zakice Ahmad kayi sallah?🙂 Idan yace eh sai kice to shikrnan naji dadi tunda kayi sallah, kadan Allah taala yace kaza_kaza_kaza akan sallah etc.


Idan beyi ba ba dukan shi zakiyi ba cikin dabara da wasa zakisa shi yayi sallah din cikin kwanciyar hankali Dadai sauran abubuwa makamantar su Babu wayewa idan kika zauna baki wasa da yaro saidai kullum fuskarki a daure😡


Wata sakaryar ma koda dariya takeyi tana hira da taga yaranta sai ta daure fuska🙄 nonsense Kina kashe kanki ne baki sani ba


Da zaran yaro yace mama sai ta daga murya tace "meyeee" to sannu sabuwar tunkiya Kin tsoratashi kince meye yace miki bakomai Kinzo kuma kina cewa Dan ubanka kasan ba komai kakirani? See this!!!


Yaro soyayya da kulawa da tarairaya yake nema A haka zakisan damuwarshi har kisan ya zaa shawo kan matsalar Amma da zaran kina hantarar shi da kyararshi zai fara kaima abokai damuwarshi A haka harsu daura shi akan mummunan hanya Allah ya sa mu dace ya tsaremu akan imanin mu ya bamu ikon tarbiyar yaran mu akan tafarkin gaskiya.


 ~By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻‍🍳~



Post a Comment

0 Comments