DALILAN DA YAKE KAWO RASHIN ZUWAN JININ AL'ADA GA YA MACE.
Gamasu bibiyarmu Susan muna cin bayanin abubuwan da ke kawo rashin zuwan jinin al'ada.
Zamuci gaba da yardar Allah.
Maganin hana daukar cikin da aka yi allura ko aka dasa su acikin jiki to dukan su suna iya hana zuwan al'ada.
Medication/ kwayoyi na wasu Rashin lafiya sun iya tsayar da jinin al'ada din mace wadannan magun gunane sn kunshi;
>>Magungunan da ake anfani dasu wajen magance matsalolin ciwon kwakwalwa (Antipsychotics drugs).
>>Magungunan jinyar cutar Sankara (cancer chemotherapy drugs).
>>Magungunan ciwon damuwa(Antidepressants).
>>Magungunan rage karfin jini(Blood pressure drugs).
Wadannan duk suna hana zuwan jinin al'ada, sai Kuma yanayin tsarin rayuwar mace yana daga cikin abubuwan dake sanadin Rashin zuwan al'ada.
1) Rashin jiki idan Akwai rama a jikin mace sosai Yana iya katse hanzarin aikin Hormones tayadda al'adar ta zata tsaya.
2) Akwai Kuma yawan jiki da Kuma yawan samun damuwa duk suna iya tsayar da jinin al'ada.
3) Akwai Kuma Hormonal imbalance Wanda wasu matsaloli ne ke Haifarwa misali ;
>(Premature menopause) Macen da tashiga matakin daina al'adar ta da wuri , dama yana farawa ne daga shekara 50 , to wasu sukanviya shiga tumma kafin shekara 40.
4) (Thyroid malfunction) matsala aikin thyroid Rashin aikin ta yadda yakamata .
5) Pituitary tumor dakuma polycystic ovary syndrome (pcos).
MATSALOLIN DA SUKA SHAFI TSARIN SASSA NA HANA HAIHUWAR MACE , SUMA SUNA HADDASA ZUWAN AL'ADA.
0 Comments