Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

SAHIHAN MAGUNGUNAN KOWANE IRIN (INFECTION) SANYIN MARA KALA-KALA



 MUHIMMAN MAGUNGUNAN INFECTION SANYIN MARA MASU KASHE INFECTION NAN TAKE


💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊


💊1). Neem wato dalbejiya maganin infection ne na haƙiƙa, ki yi garin sa ki sha tea spoon safe da yamma a cikin madara, ko kuma ki daka danyen sa ki dafa da ruwa na minti goma in ya huce ki rinƙa kama ruwa da shi safe da yamma har sai kin daina jin ƙaiƙayi kuma zuban ruwan ya tsaya. Haka nan in akwai ƙuraje sosai ki jajjaga ki zuba coconut oil ko zaitun in babu ki ɗebi zallan sa ki shafa a dukkanin wurin da kuraje suka feso na minti 30 sai ki wanke. Ki siyo oil ɗin ki rinƙa shafawa a gabanki in da ki ke jin ciwo da ƙaiƙayi, haka nan za ki iya shan tea spoon na man safe da yamma.


💊2). Malmoh maganin infection ne, yana wanko duk wani ruwan da infection ke fitarwa a jiki, yana kuma gyara vaginan mace, ki dafa shi ki sha kuma ki rinƙa kama ruwa ko zama a ciki.


💊3). Aswakin mata ko Aswakin zaki yana kashe infection da tsayar da discharge, ki dafa shi har sai ruwan ya canza kala ki sha rabin kofi safe da yamma, ko rinka shan tea spoon na garin safe da yamma da madara.


💊4). Turmeric wato kurkum yana kashe infection, ki rinƙa cin sa a abinci ko ki samu madara ki dan dafa kadan ki zuba tea spoon na shi ki sha rabin kofi safe da yamma zai mutu, zai hana wannan zuban ruwan mai wari.


💊5). Babunaj da hulba suna kashe infection a dafa kaɗan a zuba zuma a sha zai kashe infection.


💊6). Tazargade maganin infection ne na haƙiƙa, yana kashe infection, tsayar da zuban ruwa da duk wani matsalar da suka shafi ƙasan ki, ki tafasa kina sha safe da yamma har sai ciwon ya tafi.


💊7). Green tea yana kashe infection na haƙiƙa da cutuka masu yawa, ki siyo green tea ki rinka shansa ko da zafi ko da sanyi duk ba damuwa, ka da ki saka sugar sai zuma.


💊8). Bagaruwan mata yana kashe infection a dafa shi tare da tafarnuwa da kanunfari a zauna ciki ko a kama ruwa zai kashe shi ya gyara ƙamshin wurin sannan ki matse.


💊9). Lalle yana kashe infection sosai, rage budewa da wari. A dafa shi tare da kanunfari a zuba musk, tafarnuwa, da bagaruwan mata ana zama a ciki ko tsarki.


💊10). Aloe vera maganin infection ne sosai, domin kashe infection da tsayar da discharge a cire abun cikin a ɗan jajjaga a zuba ruwa ana shan kofi ɗaya da safe da yamma, kuma a rinka inserting gel din a cikin al’aura zai kashe kuraje, hana ƙaiƙayi, ɗashewa da budewa.


💊11). Ganyen rumman yana warkar da infection da tsayar da zuban ruwa mai wari da ƙarni, in an samu fruit din a sha, in ba a samu ba a nemi ganyen a sha da ruwa ko madara kullum da safe kafin breakfast.


💊12). Ganyen gwaiba maganin infection ne, ki dafa shi ki na sha sau uku a rana zai tsayar da zuban ruwa ya kuma kashe infection.


Wadannan magungunane masu kyan gaske Wanda idan kika dauki guda daya kikayi amfanidashi inshallahu matsalar infection dinki tazo karshe.






Post a Comment

0 Comments