WASU HANYOYIN GYARAN FUSKA KIYI HASKE DA FIDDA TABO DA SAMUN LAUSHIN FATA
Za a iya hadin ruwan lemun tsami da na zuma sannan a shafa a fuska ko jiki, domin inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje.
Akwai hadin ayaba da kwaiduwar cikin kwai da man zaitun. Idan aka yi wannan hadin, sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin sannan a wanke, shi ma wannan hadin domin gyaran fatar jiki da kuma na fuska ne.
Hadin ruwan lemun zaki da ruwan kwai da kuma kurkum na da matukar muhimmanci sosai domin yana taimakawa wajen gyaran fata, musamman ma ga amare.
Garin bawon lemu wanda sai an busar sannan a daka a tankade sannan a hada da ‘baking soda’ shi ma yana magance cututtukan fata sosai.
Akwai hadin ruwan kwakwa da garin bawon lemun zaki da kuma madara. Wannan irin hadin na sanya fata sulbi sosai.
0 Comments