Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKE HADA SABULUN ZUMA (HONEY SOAP) CIKIN SAUKI


 YADDA AKE HADA SABULUN ZUMA (HONEY SOAP) CIKIN SAUKI INSHALLAHU



Abubuwan buqata👇


Caustic soda gwangwani daya

coconut oil  gwangwani uku

zuma rabin gwangwani

turare of your choice essential oil



Dafarko zaki auno Caustic soda gwangwani daya sai ki jika shi da Ruwa gwangwani biyu ki juya shi har sai ya narke sai ki barshi zuwa awa 24hrs


Bayan yayi awa 24hrs sai ki dauko coconut oil dinki gwangwani 3 ki zuba a roba Mai Fadi ko girma idan ya  daskare sai ki fara narka shi idan kuma bai daskare ba shi ke nan,Bayan kin zuba coconut oil a roba sai ki dauko wannan Caustic soda da kika jika ki zuba akan coconut oil din sai ki ta juyawa har sai ya hade jikinsa kin dena ganin alamar mai Zakiga yayi kauri,xaki Dade kina juyawa kafin ya narke.


Bayan nan sai ki dauko zuma rabin gwangwani  ki zuba kita  juyawa again daganan saikisa masa  turare  saiki sake juyawa, shike nan sai ki zuba turare,seki sakaa color  kijuye a mold  saiki  rufe shi zuwa awa 24,sai ki Bude Ki barshi ya bushe.



Post a Comment

0 Comments