YADDA AKEYIN CUP CAKE CIKIN SAUKI👇🏻👇🏻
Ingredients
• Filawa/Rabin mudu
• Kwai/15
• Sugar/gwani biyu ko 1/2
• Butter simas/2
• Beaking powder
• salt/ dankadan idan kinaso
Yadda ake hadin
Dafarko Zaki dauko filawarki ki tankada ta kizubata cikin roba ko wani kwano Mai kyau sai ki dauko wata robar kizuba sugar da butter kita murzawa har sai yafara yin fari idan da hannun dama kika fara murzawa to da hannun zaki toya ba a canza hannun idan sugar da butter yafara fari saiki fasa kwai da beaking powder yadda yakamata saiki kara motsawa ya motsu sosai saiki kawo filawarki ki zuba kiyi kwabin daidai kar yayi kauri kuma kada yayi ruwa inkin kwaba saiki dauko tandar cake ko cups masu kyau ki ringa zuba ciki kina jerawa cikin oven ki rage wuta karki bari yadau tsawan lokaci karya toye zaki iyaci da lemun kwakwa ko lemun madara ko duk abinda yasamu
Aci dadi lpy
~By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳~
0 Comments