YADDA AKEYIN HADADDIYAR MEAT YAM BALLS MAI DADIN GASKE.
Doya
Nama
kwai
cornflask
maggi
spices
taruhu
albasa
garlic
Zaki dafa doya ki daka ta ki juye aroba ki soya taruhu albasa ki zuba akai kisa maggi da spices ki cakuda ta ki gutsuro doyar ki dan curata ki fadada ki zuba danbun nama acikk ki mulmule ta sai ki dan danna ta tayi kamar wainar rogo,haka har ki gama.
Ki kwaba egg da albasa da maggi ki daka cornflask ki ajje.
Ki tsoma wannan yam balls acikkn kwai sai ki sashi cikim dakakken corn flask ki soya acikin mai har kk gama
Note:zaki iya yin na dankali ma duk haka akeyi.
Amfanin soya kayan miys kafin ahada yamballs shine yana dauke gafin kayan miya kuma yafi hade jikinsa wajan balls din.
~By Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳~
0 Comments