YADDA AKEYIN ICE CANDY
Madara gari
Madaran ruwa
Suger
Fulawa
Pink colour
YADDA AKE HADAWA
Kisamu kwano kizuba madaran gyarinki da yawa ki kwaba yazama kaman na ruwa amman baso yayo kauri sosai saki daura tukunya akan wuta kizuba madaran dakika kwaba yazama na ruwa kizuba acikin tukunya kibarshi yayi zafi sosai saki samu wani kwano kizuba fulawa kadan kizuna gyaran madara akan fulawan kidauko peak milk dinki na ruwa kizuba akai ki kwaba da ruwan madaran amman da kauri kauri idan yayi saki dauko kizo kan madaran ruwanki nakan wuta kiringa zuba madaran nan akan madaran wuta har ya kari saiki ta juyawa har yayi kauri amman ba kitibar ba da ruwa ruwan zaki sauke saki juyi acikin kwano kibarshi na minti 7 saiki dauko idan yayi kudaji ki burga amman nawa tace kudajin nayi yaso yabani matsala idan kuma kinada mixsar kiyi dashi yayi smooth saiki zuba suger acikin yanda kikeson zakinshi kijuya kikuliki kai fridge na tsawon awa daya zakiga yakara kauri saki raba madaran roba biyu kisama dayan colour nawa pink nasa kadan zakisa zakiga yayi pink sosai saki dauko robobinki kizuba pink din madaran akasa sannan kizuba farin duk yanda kikeso kisa abinki saki kuli kikai fridge yayi kankara amman ba sosaiba yazaman idan kinasha kina hadawa dazuwan
Idan kikaji wajan masu siyarda kayan hadin cake kice abaki colour na wanda ake sawa a aci cream ko dectng cake na ruwa zasu baki
Kina iya fara sana,a dashi ballantana ynxu zamu shiga yanayin zafi ana ciniki.
~Chef Oum Aslam & meenat✍🏻👩🏻🍳~
0 Comments