*YADDA AKEYIN TSUMIN RAKE MAI SAUKAR DA NI'IMA EMERGENCY*
Tsumin rake shine babban sirrin masu aure koda yake akwai sassa na duniya da suka ɗauki wannan amatsayin shayi dake ƙarfafa kwayoyin haifuwa sannan su kuma mata suka riƙeshi a matsayin tsumi wanda yake mayar dasu cikin ni'ima a koda yaushe sukasha haka zalika ƙarfafa guiwa wajen saduwa,
kamar yanda naga rubutun wata mata daga yankin asiya ta ƙirashi da suna *HAƊIN ZAMAN AURE* a taƙaice dai tsumine dayake ƙarawa mace ni'ima, wanda ake shansa sau biyu safe da maraice,
rake anaso asamu koren wanda ya zama mai zaƙi sosai sai aɓare a yanyanka sannan a zuba masa ruwa a yanyanka ɗanyar citta aciki sai a yanka lemon zaƙi koda guda 1 sai kananfari wanda koda guda 4 zaiyi sai a dafa idan ruwan ya tafasa sai a sauƙe abari ya huce lokacin ya jiƙa sosai sai a matse raken sosai sannan a tace kayan sai asamu waje me kyau a ajiye maza da mata kowa zai iyasha amma ba'a ajiyeshi a cikin firji, domin ba'aso yayi sanyi, kada kisha sai kinada aure.
0 Comments