Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKU KIYAYE KARYEWAR GASHI SANNAN KI SAMUN GASHI MAI TSAWO DA SHEKI YAYI BAKI TA HANYAR AMFANI DA CASTO OIL


 YADDA AKE AMFANI DA CASTO OIL WAJEN HANA ZUBEWAR GASHI DA SAMUN TSAWO DA SHEKI GASHI YAYI BAKI


Assalamu alaikum matan gidan nan, tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a lokacin sanyi. 


Gashin kawunanmu na bukatar kulawa sosai saboda gashin mace na cikin abin da ke kara mata kyau. Akwai abubuwa da dama da suka kamata ki yi amfani da su kamar su; man zaitun da zuma da man ‘castor’ da ruwan lemun tsami da man kwakwa. Wadannan nau’o’in mai suna da inganci sosai musamman wajen kare gashi daga tsinkewa da kuma sa shi karfi da santsi da sheki.


Man Kasto (castor oil)

🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕


Man Kastor (castor oil) na taimakawa wajen gyara gashin kai a hunturu. A debo man kastor kamar cokali uku, sai ki shafa a fatar kai sannan a taje a hankali. A turara tawul har sai ya yi zafi, sannan a daura tawul din a kai na tsawon minti 15, bayan haka, sai a yi wanka. Yana hana gashi tsinkewa a lokacin hunturu.



Post a Comment

0 Comments