Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKUYI MAGANIN DANDRUFF DA ƘAIƘAYIN KAI


 MAGANIN DANDRUFF DA ƘAIƘAYIN KAI



ki jarraba wadannan zaku dace inshallahu:

- Bayan kin tsefe kan naki, Ki wankeshi da ruwan dumi wanda aka gaurayashi da Ma'u Khal. Ki barshi ya bushe sannan ki samu Man Lalle (Henna Oil) ki shafe gashin naki sosai.

Haka zaki rika maimaitawa duk bayan sati biyu (duk sanda zakiyi kitso). In sha Allahu zaki warke. Koda gashin yana karyewa zai dena. Kuma koda akwai Quraje duk zasu mutu baki daya.


- Ki samu Lalle cokali 7 ki dafashi acikin ruwa lita 2 bayan ya tafasa sai ki saukeshi ki surka sannan ki wanke Kanki sosai da wannan ruwan. Kafin nan kuma kin tanadi Man Zaitun dinki cokali 3 zuwa 5, da kuma Garin Habbatus sauda cokali 2 Ki hada Garin Habbatus sauda din da Man Zaitun din ki gaurayasu ki zuba cikin gashin naki. Ki chudanyeshi sosai. Sannan ki daure kan naki da dan-Kwali  ko leda har tsawon Awa daya ko biyu, Sannan kije ayi miki kitson.


In sha Allahu zaki rabu da wannan matsalar. Kuma koda kina da Kwarkwata duk zasu mutu. Koda gashinki yana karyewa in sha Allahu zai dena.



Post a Comment

0 Comments