YAU ZANYI BAYANI NE AKAN RUKUNIN JINI (BLOOD GROUPS)
Blood Group : Na nufin Nau'in jini ajikin Dan Adam.
NAU'O'IN JINI ;
A+, A-, B+, B- , AB+, AB- , O+, O-
NAU'O'IN JINI DA KALAN WANDA ZASU IYABAWA JINI
1) A+ Zai iya karbar jini kawai daga gurin masu ; A+, A-, O+, da O-
2) A- Zai iya karbar jini daga gurin mai ; A-, da O-
3) B+ Zai iya karbar jini daga gurin mai ; B+, B-, O+, da O-
4) B- Zai iya karbar jini daga gurin mai ; B-, da O-
5) AB + Yadace da dukkan nau'ikan jinin
6) AB- Zai iya karbar jini daga gurin AB-, A-, B-, O-
7) O+ Zai iya karbar jini daga gurin mai ;O+, da O-
8) O- zai iya karbar jini daga gurin mai O- ne kawai.
SHIN AKWAI ALAQA TSAKANIN CUTUKA ZUCIYA KAMAR HAWAN JINI DA BLOOD GROUPS❓
Tabbas, Akwai Alaqa ;
Masu Jini O- ko O+ sunada mafi qarancin na hatsarin kamuwa da cutukan zuciya.
Masu jini A+ ko A- sune suke kin masu O gurin mafi qarancin hadari
Masu Jini rukunin AB dakuma B (+ and -) sune sukafi kowa hadarin kamuwa da cutukan zuciya misalin hawan jini.
SHIN KO BLOOD GROUPS YANA ALAQA DA WASU ABUBUWA KUMA NA RAYUWAR MUTUM❓
Tabbas; Rukunin Jini (Blood Group) Yana Alaqa da Abubuwa kamar haka ;
1) Yana alaqa da cutukan dazasu iya kamaka nan gaba
2) Yana alaqa da haihuwa ko yawan barin ciki
3) Yana alaqa da Dabi'u da halaye
4) Yana alaqa da hadin aure tsakanin mijin dayadace da kai ko matar da tadace dakai
5) Yana Alaqa da irin kalan aikin qarfi ko motsa jikin daya dace dakai
6) Yana Alaqa da irin abincin dayadace dakai da lafiyarka,
Muhadu a Shiri na gaba domin Jin cikakken Bayani...
Allah ya Karo mana Lafiya baki daya.
0 Comments