*Yadda Akeyin Hadin Uwar Gida Kinfi Kankana Ruwa 🍉😋*
Wannan hadin yana sa mace ta kasance cikin ni'ima da yawan naso matukar tana shan wannan hadin kuma wanda suke shan wannan hadin ba a kwace musu miji kema ki koya kiga yanda zaki tara ni'ima.
Zaki nemi kayan hadin kamar haka;
* Kankana
* Garin kanunfari
* Garin dabino
* Kwakwa
* Madara peak
YADDA AKEYIN HAƊIN 👇
*Bayani;* Zaki samu kankana mai kyau sai ki fere samanta kiyi mata kofa a sama sai ki kawo garin kanunfari ki zuba a cikin kankanar sai ki samu garin dabino shima ki zuba a cikin kankanar sai kuma Kwakwa kwallo daya ki fasa ki zuba ruwan a cikin kankanar sannan itama kwakwar ki gurzata ta zama gari ki zuba aciki kankanar shikenan kin hada sai ki ajiyeta a waje mai tsafta kamar firige bayan awa goma sha biyar (15 hours) sai ki fara sha harya kare, yar uwa wannan hadin ba na bari bane ,na musamman ne
~Chef Oum Aslam & meenat ✍️ 👩🍳~
0 Comments