Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

BANBANCI TSAKANIN SHAWAR MACE DA TA NAMIJI. SANNAN WA YAFI WANI JIN DADIN JIMA'IN


 BANBANCI TSAKANIN SHAWAR MACE DA TA NAMIJI. SANNAN WA YAFI WANI JIN DADIN JIMA'I ?


Toh Sanin kowane dai halittar mace ta sha banban da halittar naimji.Kama daga fuskar mace ba iri daya bace da fuskar namiji, muryarta ya banbanta, kirjinta, bayanta dama gabanta duka ba irin na namiji bane.Allah ya halitto mata da sassan dake da matukar daraja da daukar hankalin namiji,sassan da ke tada shawar namiji,sassan da ke biyawa namiji da bukata,sassan da ke shayar da jinjiri (baby) da abinsha (breast feeding)har yakai ga lokacin da za a yaye shi sannan ya fara cin abinci.


Kugun mace (hips) ba irin na namiji bane,haka damutsanta (arm) sun banbanta.


Ta bangaren shawa,ita dai shawar namiji tamkar ka cinnama  kara wutane wanda nan take suke kamawa kuma nan take suke cinyewa, sabanin shawar mace wanda ita kamar an cinnawa itace wutane,a hankali yake kamawa kuma a haka suke ci har su kare,Idan muka duba anan za mu ga cewa ita mace tana bukatar lokaci mai tsawo a yayin jima'i wanda shi kuma namiji nan take a cikin mintuna biyar da tasowar shawarsa da fitarta duka a cikin lokaci kan kani.Haka kuma shi namiji dazaran yayi inzali to duk dadin ya riga ya fita(dadin yan dakikune,i.e seconds) saidai in zai sake komawa a zagaye na biyu wanda duka dai abu gudane.Amma ita mace takan iya yin inzali har sau biyu a cikin jima'i guda (multiple orgasm). Mace tana iya yin inzali kodai a sanadin gugar da zakarin namiji keyi zuwa ga belinta (clitoris) ko kuma a sanadin gamsuwar da take samu sanda zakarin namiji ke gugar wani waje a cikin farjinta da ake kira 'G-spot' (clitorial orgasm or viginal orgasm) su ne inzalin da matce keyi a yayin jima'i.


A yayinda shi kuma namiji matukar wani abu mai taushi yana gugar zakarinsa to takene zai yi inzali, kuma inzali guda yake yi.Anan,da mai yin inzali biyu koma fiye (multiple orgasm) a lokacin jima'i kima dadin yakan kai mintuna kusan biyar, da mai yin guda tilo kuma dadinsa a cikin yan seconds ya gushe, wa yafi wani jin dadi ?


Amsa anan ita ce mai yin inzali biyu ko fiye,kaga kenan mata sun fi jin dadin jima'i saidai namiji yafi shagaltuwa.


Bincike ya nuna cewa a sanadin belin dake a saman farjin mace wanda an kayi amanna cewa yana jin mugun tabi fiye da kowane waje a jikin mace(high sensitive) dan yana hade da kusan kananin jiyoji guda dubu takwas(8000 sensitive nerves ending),a lokacin jima'i muddin zakarin namiji na gugar nan wajen to mace takan ma iya fita daga haiyacinta saboda jin dadi,a yayinda shi ko namiji kan zakarinsa ke dauke da jiyoji dubu hudu (4000 nerves), kaga ashe na mace ya ninka na namiji har sau biyu.kuma duka a dalilin sune ake jin dadin jima'i.To da mai takwas da mai hudu wa yafi wani ?


Ita dai mace a duk sanda shawarta ya motsa to sai ta kasance bata da natsuwa,ta rinka mika da hamma, ga kasala, mutuwar jiki da kuma jin tamkar ana sukarsu da allura, wasunsu kan ji qai-qaiyi.


Su kuma maza zakarin su ne kan tashi akai akai,suma zasu ji sha'awa wanda kamar zasu ci babu musamman ga samarin da basada aure.


 ~____✍🏻Chef Oum Aslam meenat👩🏻‍🍳~



Post a Comment

0 Comments