Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ALAMOMIN DA MACE IDAN TA HAIHUIDAN KIKA JISU KIYI GAGGAWAN ZUWA ASIBITI


ALAMOMIN DA MACEN DATA HAIHU YAKAMATA IDAN TAJISU TAYI GAGGAWAN ZUWA ASIBITI


┈┉━┅━💕🌷💕━┅━┉┈💕━┅━┉┈💕━┅━┉┈


Duk mai jegon da bayan haihuwa koda da kwana 1 ne ballantana ace ankwana uku da haihuwa taji alamun zazzabi, ko ciwon kai, ko ciwon kirji da sauransu..... Toh lallai ta sanar ahanzarta kaita asibiti kar a kuskura! ina maimaitawa kar a kuskura! ace ai bakomi tasha paracetamol ko ace za'a nemo Maganin ulcer kurum abata babu komi. Hakan tamkar tallafawa me kokarin kashe kaine.


Sau tari a yanzu akanzo taron suna me jego ba lafiya sosai, amma taita juriyar banza saboda cutar da kai, alhalin ƙwayoyin cuta sun sami hanya ta dalilin jinin nifasi dake fita sun shiga cikin jijiyoyin jininta suna haifar matan da puerperal fever da zai kaita ga "Puerperal sepsis" yat cinta ajika tana zaton abu ne dazai zo ya shige karshe sai gawa.


Galibi wannan shike kashe Masu jego inka cire batun zubar jini bayan haihuwa, musamman bayan kwana 3 da haihuwa zazzaɓin yafi somawa domin incubation period din kenan na kwayoyin cutar, shiyasa wata sai bayan anyi taron Suna ana murna kurum aji an wayi gari wance ta Mutu, mutuwa me duka.


Kada a taɓa ɗaukar hakan da wasa, ko baka da kuɗi ranto kakaita asibiti, matukar me jego tace bata lafiya ƙasa da kwana 40 da haihuwa kar ai wasa.


Ku kuma ƙananun jami'an lafiya dake bibiyar rubutuna koda yaushe kusa wannan cikin kanku, kar me jego tace:-


- Tanajin kasala,

- Kanta na ciwo

- Zazzaɓi

- Fitar farin ruwa ko jini me ɗoyi

- Ciwon Mara

- Zafin fitsari

- Ko har yau girman cikinta yana nan da sauransa kamar bata haihu ba ko kamar da sauran jariri aciki


Kuce zaku bata maganin rage zogi kurum ku sallameta, ko kuwa kuce zakui gwajin Malaria don haka in ya nuna Negative saide ku bata pain reliever, ko kuma in akai kicibis ga Malaria positive kuce iya Malaria ke damunta...


Kuke buɗe tunaninku sosai for differentials diagnosis, kada ace komi inya haɗo da ciwon kai kurum Malaria ko Bp, ko Typhoid ne. 


duk Macen da kukaji tai muku korafin ɗaya ko biyu daga waɗancan alamun na sama kai tsaye kuyi treating dinta for puerperal infection muddin me jego ce, domin hakan nada alaka da haihuwarta. Mai jego itace wadda bata euce kwana 42 da haihuwa ba. Don haka koda tai wata da haihuwa duk da haka tana cikin hatsari harna zubar jini. 


Ya rage naku kuje kui biyayya ga manyanku da kuke aiki karkashinsu, su ilmantar daku magungunan da alluran da ake amfani dasu wajen addressing din matsalar, don ba kowanne antibiotics ake basu ba, in suma basu sani ba toh kuje sahihan journals na obstetrics and gynecology kui binkice ku ilmantar da kanku bawai google ba. Wannan lamari ne da kan zamo Medical Emergency. 


Wannan tasa ko ɓari Mace tayi sai anbata Magungunan antibiotics, hakama bayan haihuwa domin rigakafi koda kwayoyin cutar sun makale to zai magancesu kafin sui karfin da zasu shiga jini tunda ido bai iya ganinsu.


AMMA wasu Marasa tunanin cikin Mata basa sha, ko in sun fara sai su bar sha tun kafin ya qare... toh masu irin wannan ku kuka da kanku, Domin ba zubar jini ne kurum abin tsoro ba bayan haihuwa.


In muka kiyaye wannan zamu taimaka wajen rage wasu mace-macen na masu haihuwa. 


Allah yasa mu dace.



Post a Comment

0 Comments